‘Rayuwarmu a jihohin dokar ta-baci’

A halin da ake ciki dai jama’ar jihar Adamawa suna  gudanar da harkokinsu cikin tsanaki,kodayake maza na neman komawa mata ,inda suke shiga gida da wuri,yayin da matan aure ke murna da ganin mazajensu a gida, ba tare da sun fita hirar dare ba.su ma  ‘yan mata suna kokawa, ‘’Ba mu ji dadin dokar hana […]

‘Rayuwarmu a jihohin dokar ta-baci’
‘Rayuwarmu a jihohin dokar ta-baci’

A halin da ake ciki dai jama’ar jihar Adamawa suna  gudanar da harkokinsu cikin tsanaki,kodayake maza na neman komawa mata ,inda suke shiga gida da wuri,yayin da matan aure ke murna da ganin mazajensu a gida, ba tare da sun fita hirar dare ba.
su ma  ‘yan mata suna kokawa, ‘’Ba mu ji dadin dokar hana fitar nan ba, domin samari yanzu ba sa zuwa hira sai dai ta waya,’’ a cewar Halima Musa,wata budurwa a Jimeta cibiyar gwamnatin Jihar Adamawa.
Gwamnan jihar Adamawa  Murtala Nyako cewa ya yi,  ‘’A gaskiya mun yi mamaki da wannan dokar ta-bacin da aka kakaba  mana,kowa ya sani cewa mu a nan Adamawa barayi ne suka addabe mu, kamar sauran jihohi. Amma sai mu yi hakuri mu zama masu biyayya kuma mu cigaba da yin addu’a ga wadanda ke nemanmu da sharri.’’
Ya yi wannan bayanin a lokacin da yake yi wa al’ummar jiharsa  bayani jim kadan da kafa dokar  ta-bacin da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi wa wadansu jihohi uku da suka hada da Borno daYobe da kuma Adamawa.
Kamar gwamnan jihar, su ma sauran mutanen jihar bakinsu kusan ya zo daya game da dokar, sai dai wadanda ke hamayya da Nyako, wato ‘yan bangaren shugaban jam’iyyar PDP na kasa Bamanga Tukur  suna ganin dokar ta yi daidai, har wasunsu na zargin gwamnan da cewa sakacinsa ne ya jawo kafa dokar.
Gwamnatin jihar ta bakin daraktan watsa labarai na  gidan gwamna,Malam Ahmad Sajo,ta yi fatali da masu irin wannan suka, ciki har da shugaban jam’iyyar PDP  bangaren su Bamanga Tukur, Cif Joel Madaki. ‘’ Abun ta kaici ne a ce wadansu na son siyasantar da rayuwar al’ummar wannan jiha, a gaskiya da mamaki,ya kamata jama’a su rika yin adalci  ga duk abun da za su furta,’’ inji Ahmad Sajo.
Sojoji sun kafa dokar hana fita daga karfe shida na maraice zuwa shida na safe, a daidai lokacin da jami’an tsaro ke cigaba da farautar  ‘yan bindiga,kodayake daga baya an sasassauta dokar a ranar  Talatar da ta gabata.
Ra’ayoyi sun bambanta
Aminiya  ta kewaya jihar  don jin ra’ayoyin jama’a kan wannan lamari, ganin cewa wadansu na ganin cewa a jihar  Adamawa ana  fakewa da guzuma ce kawai don a harbi karsana, musamman ganin irin kai ruwa rana da aka yi ta yi a tsakanin kusoshin PDP na jihar da kuma batun kujerar gwamnan jihar a shekarar  2015.
Alhaji Hussaini Bello Gambo, wanda yake daya daga cikin masu taimaka wa Gwamna Murtala Nyako, ya bayyana cewa, “wannan siyasa ce kawai, don idan ka dauki abubuwan da suke faruwa a wadansu jihohi irinsu Borno da Filato da Yobe da Nasarawa da Wukari da kuma Ibbi a Jihar Taraba, to babu wani dalilin da zai sa a kafa wannan doka a Adamawa, don mu babu abin da yake faruwa a nan. Don haka wannan siyasa ce, wanda kuma bai kamata a ce shugaban kasa ya yi amfani da dokar ta-baci don cim ma burinsa ba.”
Shi kuwa Alhaji Sani mai Gwal cewa ya yi, “Ni a ganina, a sakamakon Gwamna Nyako ya ki ya bari sojoji su rika zaluntar jama’a kamar yadda suka ga dama ne ya sa shugaban kasa ya kafa dokar don kawai ya samu damar cim ma burinsa, su kuma sojoji su zalunci mutane yadda suke so. Saboda haka, ya kamata dattawan jihar nan su fito su kalubalanci wannan matakin da shugaba Jonathan ya dauka wanda ba zai haifar wa Jihar Adamawa da da mai ido ba.”
Su kuwa Garba Manu da Rebaren Phineas Padio  ra’ayinsu ya dan sha bamban da na saura, inda suka ce matakin da aka dauka yana da bukatar yin dogon nazari kafin a yanke hukunci a kai. “To, wannan doka ya danganta da yadda ka fahimta, saboda yanayin yadda harkar tsaro ta zama. Ta yiwu jami’an tsaro akwai abin da suka sani na sirri, amma dai muna son zaman lafiya. Kuma ina ganin siyasa ta taka rawa a ciki, don ba a taba kafa doka awa 24 don matsalar tsaro a Adamawa ba, to me ya sa za a kafa dokar ta-baci? To muna fatan Allah Ya kiyaye, muna son abin da duk zai inganta tsaro da zaman lafiyar al’umma, don haka wannan al’amari muna fatan alheri a cikinsa.”
Haka kuma harkokin yau da kullum kamar kasuwanci da aikin gwamnati  da harkokin bankuna da na manema labarai sun tsaya cik a Jahar Yobe a sakamakon katsewar layukan sadarwa na wayar tafi-da-gidanka da kamfanonin sadarwa masu zaman kansu irin su MTN, da AIRTEL da GLO da ETISALAT  suka yi a dukkan fadin jahar, wanda ya haifar da nakasu ga al’amuran  yau da kullum.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, wannan hali da al’ummar jihar  suka samu kansu a ciki na katsewar dukkan layukan sadarwa da suke zargin dokar ta-bacin da aka sanya ne ta haifar musu, ya haddasa matsaloli masu tarin yawa.
Wani dan kasuwa da ya nemi da a boye sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewa, tun da ya fara hada hadar kasuwancinsa kusan kimanin shekaru 8 ke nan bai taba samun kansa a cikin kunci ba kamar wannan lokacin, kasancewar akasari yana amfani ne da wayarsa ya ce a aiko masa da kaya daga Kano, amma yanzu ala tilas sai yay i tattaki har zuwa Kano kafin ya samu biyan bukata, wanda hakan babbar asara yake  haifar masa, kuma har ya zuwa yanzu ba su san yaushe ne wannan matsala za ta kau ba.
Don haka dan kasuwar ya yi roko ga duk wadanda suka haddasa musu wannan irin matsala da su yi wa Allah su dawo musu da hanyoyin sadarwarsu don kar abubuwan su yi musu yawa, domin da kuncin rayuwar da wannan doka ta sa su ne za su ji, ko kuwa da matsalar katsewar hanyoyin sadarwa? ganin cewa da su ne suke amfani wajen gudanar da harkokinsu na kasuwanci.
Shi ma wani ma’aikacin gwamnati a bayanin da ya yi wa Aminiya game da irin matsin da ya samu kansa a ciki dangane da matsalar katsewar harkokin na sadarwa, cewa ya yi shi babban abin da ke ci masa tuwo a kwarya shi ne yadda ala-tilas  ya sayar da kadararsa a wulakance don sayan  kayayyakin abinci  duk kuwa da cewa yana da kudi a banki amma babu damar cire su saboda babu hanyar sadarwar da bankin ke amfani da shi.
Wannan matsala dai ta katsewar harkokin sadarwa hatta  manema labarai ma ta shafe su, kasancewar dukkan hanyoyin da suke bi don aika sakonninsu sun samu nakasu ala- tilas sai su je gidan gwamnati ko kuma su je jahar Bauchi kafin su aika sakonninsu.
Baya ga matsalar harkokin sadarwa, akwai kuma ta ‘yan gudin Hijira daga wuraren da ake tunanin dakarun  da aka tura su don tabbatar da wannan doka suka fara kai samame, musamman a Jahar Borno sun fara kwararowa zuwa garin Damaturu don neman mafaka, duk da cewa garin na Damaturu ma yana cikiin wannan hali na dokar  ta-baci, wanda hakan ya kara yawaitar jama’a  a garin.
Daga Maiduguri kuwa, wani dereba da ke zirga-zirga a tsakanin Abuja da Maiduguri ya bayyana wa BBC cewa, ba kamar yadda ake bayyana cewa harkoki sun tsaya cik ba, ana hada-hada a garin kuma motocin haya suna shiga da fita garin.