Rayuwata na cikin hadari – Gwamna Ameachi
Gwamnan Jihar Ribas Cif Rotimi Ameachi ya ce rayuwarsa tana cikin haxari tun bayan da aka kammala zaven Qungiyar Gwamnoni ta Najeriya inda a zaven ya samu quri’a 19; abokin adawarsa Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang ya samu quri’a 16.Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a bikin Ranar Yara a garin Fatakwal […]
Gwamnan Jihar Ribas Cif Rotimi Ameachi ya ce rayuwarsa tana cikin haxari tun bayan da aka kammala zaven Qungiyar Gwamnoni ta Najeriya inda a zaven ya samu quri’a 19; abokin adawarsa Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang ya samu quri’a 16.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a bikin Ranar Yara a garin Fatakwal a ranar Litinin da ta gabata.
Tun bayan zaven qungiyar gwamnonin aka riqa samun cece-kuce inda kuma a yanzu jam’iyyar PDP ta dakatar da shi bisa zargin ya karya kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Da yake jawabin kan dakatar da shi da PDP ta yi ne sai ya ce: “Ba a yi mini adalci ba, domin ba a ba ni damar na kare kaina ba. Hakan kuma bi-ta-qulli ne a siyasa. Abin da nake da masaniya a kai shi ne, sun yi wata ganawa yau, washegari kuma suka sanar sun dakatar da ni, wannan ba adalci ba ne.”
Idan ba za a manta ba dai jam’iyyar PDP ta bakin mai magana da yawunta Cif Olisa Metuh ya ce an dakatar da Ameachi ne sakamakon zaman gaggawa da Kwamitin Aiwatarwa na jam’iyyar ya yi, sannan an yi amfani da qorafin da aka shigar wa jam’iyyar ne wanda ake zargin Ameachi ya karya dokar jam’iyyar PDP ta 58 1(a) da (b) da (h) da kuma (m).
Qorafin ya zargi Ameachi da cire majalisar zartarwa ta Qaramar Hukumar Obiakpor da ke jiharsa.
Bayan dakatarwar a yanzu an naxa kwamitin mutum 11 don su gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa Ameachi. Shugaban kwamitin shi ne, Joe Kyari Gadzama