Rayuwata na cikin hadari —Hadiza Gabon

Gabon ta bayyana haka ne a zaman sharia’ar da wani ya kai ta kan taki ta aure shi bayan ya kashe mata N396,000

Rayuwata na cikin hadari —Hadiza Gabon

Hadiza Gabon

Fitaccitar jarumar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon, ta yi ikirarin cewa rayuwarta na cikin hadari saboda yadda ake satar fita da ita daga kotu duk lokacin da aka zauna sauraron shari’arta. 

Jarumar ta yi wannan bayani ne ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani Jibril, a gaban wata kotun shari’ar Musulunci a Kaduna.

Lauyan na bukatar kotun ta yafe wa jarumar halartar zaman sauraron karar da aka kai ta, tun da tana da wakilci.

Barista Mubarak ya ce tabarbarewar tsaro ya sa Hadiza Gabon cikin rashin kwaciyar hankali da fargabar abin da ka iya faruwa da rayuwarta idan ta ci gaba da halartar zaman kotun.

Lauyan ci gaba da cewa duk lokacin da Gabon ta halarci zaman kotun, sai dai a yi satar fita da ita.

“Rayuwata na cikin hadari, rayuwarta na cikin hadari. Rayuwar mai karar ma na cikin hadari. Ba mu san wa ke bibiyar wannan sharia’ar ba a kafofin sada zamunta ba.

“[Idan ba a yi hankali ba] za mu iya ganin mutane dauke da bindigogi domin su sace mu.

“Wannan ita ce damuwarmu ba wannan shari’ar ba,” in ji Barista Mubarak Sani Jibril.

Lauyan mai kara, Barista Naira Murtala, ya ki yarda da rokon lauyan jarumar, yana mai ikirarin cewa dole ne ta ci gaba da halartar zaman kotu.

Alkali Rilwanu Kyaudai, ya tabbatar musu da cewa kotun za ta yi la’akari da lafiyar mai kara da wacce a ke kara a zamanta na gaba.

Hadiza Gabon ta halarci zaman kotun ne a ci gaba da sauraron karar da wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa ya kai karar ta a bisa zargin ta ki ta aure shi bayan ya kashe mata kudi Naira 396,000.