Real Madrid: Kulob mai ’yan wasa mafiya tsada a duniya

Kulob din Real Madrid da ke kasar Sifen ya zama kulob mai ’yan wasa mafiya tsada a duniya bayan jumullar kudin da aka sayo ’yan wasan kulob din ta kama Fam miliyan 533 da dubu 800 (daidai da Naira biliyan 88 da dubu 770.Aminiya ta gudanar da bincike a kan ’yan wasan kulob din, sannan […]

Real Madrid: Kulob mai ’yan wasa mafiya tsada a duniya

Kulob din Real Madrid da ke kasar Sifen ya zama kulob mai ’yan wasa mafiya tsada a duniya bayan jumullar kudin da aka sayo ’yan wasan kulob din ta kama Fam miliyan 533 da dubu 800 (daidai da Naira biliyan 88 da dubu 770.
Aminiya ta gudanar da bincike a kan ’yan wasan kulob din, sannan ta hada muku jumullar kudinsu. Kulob din Barcelona ne na biyu a duniya inda jumullar ’yan wasan kulob din ta kama Fam miliyan 371.
’Yan wasan gaba:
Kulob din ya sayo Cristiano Ronaldo a kan Fam miliyan 80 da Gareth Bale a kan Fam miliyan 85 da James Rodriguez  a kan Fam miliyan 71 da kuma Kareem Benzema a kan Fam miliyan 27, inda jumullar kudinsu ta kama Fam miliyan 263.
’Yan wasan tsakiya:
Akwai dabi Alonso wanda aka sayo a kan Fam miliyan 30 da Luka Modric a kan Fam miliyan 33 da Isco a kan Fam miliyan 24 da Toni Kroos a kan Fam miliyan 24 da Illarramadi a kan Fam miliyan 25.5 da Di Maria a kan Fam miliyan 20 da Sami Khedira a kan Fam miliyan 11, jumullar ta kama Fam miliyan 167 da dubu 500.
’Yan wasan baya:  
Jumullar kudin ’yan wasan baya: Fabio Coentrao (Fam miliyan 24) da Pepe (Fam miliyan 24) da Sergio Ramos (Fam miliyan 21) da Mercelo (Fam miliyan 7) da barane (Fam miliyan 8) da Arbeloa (Fam miliyan 3 da dubu 500) ta kama Fam miliyan 92 da dubu 500.
Masu tsaron gida:
Jumullar masu tsaron gida, bayan an hada kudin da aka sayi Lopez (Fam miliyan 2 da dubu 800) da Keylor Nabas (Fam miliyan 8) ta kama Fam miliyan 10 da dubu 800.
Aminiya ba ta gano hakikanin kudin Casillas da dan wasan gaba Jese ba.
Aminiya ta hada kudin ’yan wasan gaba (Fam miliyan 263) da na tsakiya (Fam miliyan 167 da dubu 500) da na ’yan baya (Fam miliyan 92 da dubu 500) da na masu tsaron gida (Fam miliyan 10 da dubu 800), inda jumullar kudin ta kama Fam miliyan 533 da dubu 800 daidai da Naira biliyan 88 da dubu 770.
A Zayyanar farko Aminiya ta yi hasashen jumullar kudin ’yan wasan da za su rika fara wasa idan babu matsalar rauni ko rashin lafiya a bana, ta kama Fam miliyan 400 da dubu 800. Ba lallai ne hasashen ya tabbata ba. A zayyana ta biyu kuma, Aminiya ta kawo muku sauran ’yan wasan kulob din da kuma kudinsu.  
A ranar Talata ne Real Madrid ta lashe kofin Super Cup bayan ta lallasa kulob din Sebilla da ke kasar Sifen da ci 2-0. Cristiano Ronaldo ne ya ciwo wa Real Madrid duka kwallayen biyun.