Real Madrid ta fara yunkurin saye dan kwallon Jubentus Albaro Morata
Kulob din Real Madrid na Sifen ya fara yunkurin sake sayo dan kwallon da ya sayar wa kulob din Jubentus na Italiya a bara mai suna Albaro Morata. Albaro Morata dai ya haskaka a kakar wasa ta bana ne bayan ya fitar da Madrid a gasar zakarun kulob-kulob na Turai inda ya zura kwallaye biyu […]
Kulob din Real Madrid na Sifen ya fara yunkurin sake sayo dan kwallon da ya sayar wa kulob din Jubentus na Italiya a bara mai suna Albaro Morata.
Albaro Morata dai ya haskaka a kakar wasa ta bana ne bayan ya fitar da Madrid a gasar zakarun kulob-kulob na Turai inda ya zura kwallaye biyu a ragar Madrid a gida da waje, da hakan ya sa aka fitar da Madrid a gasar.
Sannan dan kwallon ne ya rama wa Jubentus kwallo a ragar FC Barcelona a wasan karshen da suka yi a makon jiya kafin daga bisani Barcelona ta samu nasara a wasan da ci 1 da 3.
A bara ne Madrid ta sayar da Morata ga kulob din Jubentus a kan Yuro miliyan 22 amma da sharadin Madrid za ta iya sake sayensa a kan Yuro miliyan 30 ko sama da hakan idan bukatar hakan ta taso. Wannan ta sa kulob din ya fara yunkurin amfani da wannan dama don sake sayo Morata musamman ganin yadda kulob din yake fama da matsalar dan kwallon gaba.
Hasalima wasu magoya bayan Madrid tuni suka fara kiran a sayar da Karim Benzema don a maye gurbinsa da Morata a kakar wasa mai zuwa.