Real Madrid ta haye teburin La Liga bayan doke Barcelona

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta karbi bakwanci Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona inda ta  lallasa ta da ci 2-0. Wasan wanda aka buga a filin wasa na Santiago Bernabeu, ita ce zagayen karshe a wasan El-Classico a gasar La Liga ta bana. Real Madrid ta samu nasarar ne ta hannun ‘yan wasanta Vinicius […]

Real Madrid ta haye teburin La Liga bayan doke Barcelona

Vinicius Junior

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta karbi bakwanci Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona inda ta  lallasa ta da ci 2-0.

Wasan wanda aka buga a filin wasa na Santiago Bernabeu, ita ce zagayen karshe a wasan El-Classico a gasar La Liga ta bana.

Real Madrid ta samu nasarar ne ta hannun ‘yan wasanta Vinicius Junior da kuma Mariano Diaz, wanda shi ne karon farko da Madrid din ta samu nasara a gidanta akan Barcelona tun shekara ta 2014.

Zagayen farko na wasan da aka buga a filin wasa na Camp Nou, an tashi ba kare bin damo.

Yanzu dai Real Madrid ta dare kan teburin La Liga da maki 56, inda ta bada tazarar maki daya sama da abokiyar hamayyarta wato Barcelona wacce ke da maki 55.

Za’a dai sa ido aga waye zai samu nasarar lashe gasar a bana.