Real Madrid ta lashe Gasar Zakarun Turai karo na 15
Real Madrid ta zamo ƙungiya ta farko da ta taɓa lashe gasar sau 15 a tarihi.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta lashe Gasar Zakarun Turai (Champions League), karo na 15 a tarihinta.
Madrid ta doke Dortmund a wasan karshe na gasar wanda aka yi a filin wasa na Wembley da ke Birtaniya.
- Wani mutum ya sayar da ’yarsa kan miliyan 1.5 a Bauchi
- Alhazan Najeriya su guji sayar wa takari ‘uniform’ — NAHCON
Ƙwallon da ɗan wasan bayan Real Madrid, Dani Carvajal ya zura a minti na 74 da kuma wadda Vinicius Junior ya zura a minti na 82 ne, suka bai wa ƙungiyar damar sake kafa wani sabon tarihi a gasar.
Dortmund dai ba ta taɓa lashe gasar ba, inda a baya ta sha kashi a hannun Bayern Munich da ci ɗaya mai ban haushi a shekarar 2013.
Gasar Zakarun Turai dai ta zama gasar da Real Madrid ta gagara a ciki, inda ta ke ci gaba da yin warkajaminta.