Real Madrid ta raba gari da Xabi Alonso

Madrid ta maye gurbin kociyan da tsohon ɗan wasanta, Alvaro Arbeloa.

Real Madrid ta raba gari da Xabi Alonso

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Xabi Alonso, watanni takwas kacal bayan ƙulla yarjejeniya da tsohon ɗan wasan nata.

Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da fitaccen ɗan jaridar nan kan harkokin tamaula, Fabrizio Romano ya wallafa a shafinsa na X.

Aminiya ta ruwaito cewa, sallamar kociyan na zuwa ne kwana guda bayan rashin nasarar da ƙungiyar ta yi a hannun abokiyar hamayyarta Barcelona a wasan ƙarshe na Spanish Super Cup.

Real Madrid ta bayyana cewa rabuwa da kocin mai shekara 44 ta faru ne bisa fahimtar juna tsakanin ɓangarorin biyu, ƙasa da awanni 24 bayan Barcelona ta doke ta da ci 3-2 a wasan da aka buga a birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce Xabi Alonso zai ci gaba da kasancewa abin ƙauna da girmamawa ga masoyan Real Madrid, tana mai bayyana shi a matsayin waɗanda suka shiga tarihin ɗaga martabar ƙungiyar.

Tuni dai ƙungiyar ta maye gurbin kociyan da tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Alvaro Arbeloa.

Arbeloa ya shafe shekaru yana horarwa a makarantar matasa ta Real Madrid tun daga 2020, inda ya samu nasarori da dama, ciki har da lashe kambu uku a kakar 2022/2023 tare da ƙungiyar matasa ta Juvenil A.

Arbeloa ya murza leda a Real Madrid daga 2009 zuwa 2016, inda ya lashe manyan kofuna takwas, sannan ya kasance cikin tawagar ƙasar Sifaniya da ta lashe Kofin Duniya na 2010 da kuma kofunan Turai biyu a 2008 da 2012.