Real Madrid ta tallafa wa yaran da yakin Ukraine ya mayar ’yan gudun hijira

Rahotanni sun bayyana yadda ake ci gaba da samun yara ‘yan gudun hijira a Ukraine.

Real Madrid ta tallafa wa yaran da yakin Ukraine ya mayar ’yan gudun hijira

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ba da kyautar Yuro miliyan daya domin tallafa wa kananan yara da yakin Rasha da Ukraine ya mayar ’yan gudun hijira.

Wannan na zuwa ne bayan Majalisar Dinkin Duniya ta ce yara kanana kimanin miliyan daya da dubu 400 ne suka tsere daga Ukraine, tun bayan da Rasha ta kaddamar da yaki kan kasar.

Tun farkon ballewar yakin kungiyoyin kwallon kafa a duniya suka shiga nuna alhininsu da goyon baya ga Ukraine.

Sabon rahoton da Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta fitar a ranar Talata, ya nuna mutum sama da miliyan uku ne suka tsere daga Ukraine kuma kusan rabinsu kananan yara ne.

Kakakin Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) James Elder, ya shaida wa manema labarai a birnin Geneva cewa a kowace rana cikin kwanaki 20 da suka wuce a Ukraine, yara akalla 70,000 ne ke zama ’yan gudun hijira.

A takaice dai kididdiga ta nuna cewa yaro daya ke zama dan gudun hijira duk bayan dakika daya a Ukraine.

Elder, ya jaddada cewa yakin na Rasha da Ukraine na ci gaba da kamari tare da mummunan halin da dubban miliyoyin mutane ke rayuwa ta hanyar tagayyara su, tashin hankalin da rabon da a ga irinsa a nahiyar Turai tun lokacin Yakin Duniya na Biyu.