Rediyon Muryar Amurka ya yi kuskure

Edita ka ba ni dama in yi tsokaci game da labarin da na karanta a jaridar Aminiya ta ranar 9-15/10/2-156 shafi na 5, inda aka ce “rediyon Muryar Amurka (bOA) ta karrama ma’aikatan sashen Hausa.” Haqiqa ni a ganina ba a yi adalci ba, wajen karramawar. Dalilina kuwa, shi ne, ai ya kamata a ce […]

Rediyon Muryar Amurka ya yi kuskure
Rediyon Muryar Amurka ya yi kuskure

Edita ka ba ni dama in yi tsokaci game da labarin da na karanta a jaridar Aminiya ta ranar 9-15/10/2-156 shafi na 5, inda aka ce “rediyon Muryar Amurka (bOA) ta karrama ma’aikatan sashen Hausa.” Haqiqa ni a ganina ba a yi adalci ba, wajen karramawar. Dalilina kuwa, shi ne, ai ya kamata a ce Hajiya Halima Jimrau ce ta farko, Ibrahim Alfa Ahmad na biyu, kuma Jimmai Ali ta uku. Wadannan su ne a ganina suka fi kowa shirye-shirye masu fadakarwa a gidan rediyon. Misali:

1. Hajiya Halima, ita ce da noma tushen arziki, a qasashen duniya ke tunqaho da noma kuma yanzu da man feturt ke neman bacewa a duniya dole qasashe irin su Najeriya da Nijar da Chadi da sauransu su koma “naduqe tsohonj ciniki, kowas ya zo duniya kai ya tarar.” Halima tana nishadantar da masu sauraron gidan rediyon wajen filin a bari ya huce da sauran shirye-sgiryenta masu muhimmancin gaske.
2. Ibrahim Alfa Ahmad jigo ne a sashen Hausa na Muryar Amurka filayensa da tafiyar lafiya da yake yi sun cancanci a cira masa tutwa ban da fadakarwa, yana sada zumunci, wanda “addinin Musulunci ya qarfafa.”
3. Hajiya Jimmai Ali da Likitanta suna taimaka wa mutanen karkara wajen fadakar da su kan cututttuka da suka addabi jama’a irin su Qanjamau da Tinjere da Tsargiya da sauransu. Ai a duniya lafiya wani abin alfahari ce. Saboda haka akwasi kura-kurai wajen zaben gaziqan ma’aiakatanku, kada ku manta mu masu sauraronku shekara da shekaru ya kamata ku nemi shawararmu kafin ku yanke wannan hukunci.
Ina fatan za ku yi la’akari da wannan muhimiyar shawara tawa. Don na kai shekaru fiye da 20 ina saurarenku dare da rana, kuma zan iya alqalanci irin wannan.
Daga Sule Musa Dutse, Akwatin Gidan waya 51, Dutse, Jihar Jigawa