Reese Witherspoon ta zama jarumar fim mafi arziki a duniya

Kudinta ya kai Dala miliyan 400 kimanin N165bn da hannun jarin N86bn.

Reese Witherspoon ta zama jarumar fim mafi arziki a duniya

Reese Whiterspoon. (Hoto: Tinseltown na shutterstock)

Tauraruwar fina-finan Hollywood Reese Witherspoon ta zama jaruma mafi arziki a duniya inda a yanzu yawan kudinta ya kai Dala miliyan 400 (kimanin Naira biliyan 165).

Reese, mai shekara 45, ta taka wanna tudun ne bayan sayar da wani yanki na kamfaninta na shirya fina-finai mai suna Hello Sunshine a kan Dala miliyan 900 (kusan Naira biliyan 370).

Tsoffin shugabannin shirya kamfanin fina-finai na Disney, Kevin Mayer da Tom Staggs masu rukunin kamfanin Blackstone ne suka sayi hannun jari a kamfanin na Hello Sunshine.

Reese, wadda ta taka rawa a fim din ‘Legally Blonde’ tana daga cikin jarumai mafiya kudi a masana’antar Hollywood.

Ana biyan ta akalla Dala miliyan daya a duk sati na shiryawa da kuma fitowa a shirin tattaunawa na ‘The Morning Show’ a tashar Apple TV+.

Tana kuma karbar miliyoin daloli na shiryawa ko fitowa a fina-finan Hollywood da kuma tallace-tallace.

Jaridar Forbes ta kiyasta cewa yawan kudin jarurmar mai ’ya’aya uku ya kai Dala miliyan 400 (kimanin Naira biliyan 165).

Karin kudin da ta samu na nufin Reese, wadda ta lashe kyautar Oscar saboda rawar da ta taka a fim din ‘Walk The Line’ ta kara tsaga ga duk kamfanin da zai dauke ta ta fito a shirye-shiryen talabijin ko fina-finai.

Karfin Reese yanzu a Hello Sunshine

Duk da cewa yanzu Kevin Mayer da Tom Staggs ne ke da hannun jari mafi yawa a kamfanin, amma Reese Witherspoon na da kashi 18 cikin 100, wanda kimarsu ta kai Dala miliyan 120 (kimanin Naira biliyan 86.4).

Za kuma ta ci gaba da kasancewa a cikin masu kula da harkokin yau da kullum na kamfanin.

Bugu da kari, ita kadai ta tashi da tsabar kukdi Dala miliyan 120 (kimanin Naira 49.4 biliyan) bayan an cire haraji daga kudin da Kevin Mayer da Tom Staggs suka biya na kusan kashi 40 cikin 100 na hannun jarin Hello Sunshine.

Sauran masu hannun jari a Hello Sunshine sun hada da kamfanin AT&T da kuma Emerson Collective, mallakin Laurene Powell Jobs.

Reese Whiterspoon.
Reese Whiterspoon a lokacin wani biki. (Tsohuwar ajiya daga Reuters)

Farin cikin Reese

A sakon da ta wallafa shafinta na Instagram, jarumar ta ce. “Yau babbar rana ce”.

“Na fara kamfanin Hello Sunshine ne domin sauya tunanin da mutane sukke kallon mata a kafafen yada labarai.

“A ’yan shekaru da suka wuce mun ga irin nasarori da muka samu wajen cim ma manufofinmu ta litattafai da fina-finai da shirye-shiryen talabijin da kuma dandalin sadar da zumunta.

“Yau mun samu babban cigaba daga ta hanyar hadewa da Blackstone Inc., wanda zai ba mu damar fito da sabbin labarai masu ma’ana da tasisi game da rayuwar mata a fadin duniya,” inji Reese Whiterspoon. 

Ta ci gaba da cewa, “Ina matukar alfahari da ma’aikatanmu da suka kai mu ga wannan nasara, ina kuma farin cikin aiki tare da Blackstone da Kevin Mayer da kuma Tom Staggs domin fadada kamfaninmu na yada labarai na zamani.

“Sun tsaya kai da fata domin taimaka wa manufarmu ta karfafar mata su zama abin alfahari.”

Kafa kamfanin Hello Sunshine

A shekarar 20216 Reese ta kafa kamfanin Hello Sunshine wanda ya karkata wajen samar da shirye-shiryen da suka danganci mata. 

Manyan shirye-shiryen kamfanin da suka fi samun nasara da tashe sun hada da ‘Big Little Lies’ da kuma ‘The Morning Show’.

Mujallar Wall Street ta Amurka ta tabbatar da kulla cinikin kuma ta ce Reese za ta ci gaba da kasancewa a kwamitin daraktocin kamfanin.

Ba a bayyana sharudan cinikin ba, amma ta tabbata cewa kimar kamfanin Hello Sunshine ya kai Fam miliyan 650.