Remi Tinubu ta bayar da tallafin buhunan shinkafa 1,000 ga Kiristocin Yobe
Uwargidan Shugaban ƙasar ta yi hakan ne don tallafawa membobin Ƙungiyar Kiristoci don bikin Kirsimeti.
Ƙungiyar Kiristocin Arewacin Najeriya reshen jihar Yobe ta samu tallafin buhunan shinkafa 1000 daga Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu.
Uwargidan Shugaban ƙasar ta yi hakan ne don tallafawa membobin Ƙungiyar Kiristoci don bikin Kirsimeti.
- Yunwa da gazawar gwamnati ne sanadin turmutsutsi wajen rabon abinci — Kukah
- Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu
Dokta Yahaya Galo, ɗaya daga cikin mahalarta taron, ya shaida wa manema labarai a Cocin da ke Potiskum cewa za a raba shinkafar ga Kiristoci ba tare da la’akari da ɗarikun su ba.
“Muna godiya ga Sanata Tinubu da irin wannan karamcin kuma muna addu’ar Allah Ta’ala ya taimaka musu har tsawon zamansu a ofis.” in ji shi.
Yahaya ya yi kira ga sauran masu riƙe da madafun iko su ma su riƙa kyautatawa al’ummomin su musamman a lokuta irin haka don sa musu farin ciki a zukatan su.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin, wanda ya yi magana a madadin fastoci da masu wa’azin bishara da suka yi ritaya a jihar, Usaku Yaro Kaku, ya yaba wa Sanata Oluremi Tinubu bisa wannan gudunmawar da ta sanya a fuskar Kiristocin jihar Yobe.