Ribadu ya yi musayar zafafan kalamai da Fadar Shugaban kasa
Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati kuma dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar ACN a zaben 2011, Malam Nuhu Ribadu ya yi musayar zafafan kalamai da Fadar Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, inda Ribadu ya bayyana gwamnatin Jonathan da jirgin da ruwa ya ci, yayin da Fadar Shugaban kasar ta […]
Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati kuma dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar ACN a zaben 2011, Malam Nuhu Ribadu ya yi musayar zafafan kalamai da Fadar Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, inda Ribadu ya bayyana gwamnatin Jonathan da jirgin da ruwa ya ci, yayin da Fadar Shugaban kasar ta bakin Kakakinta Reuben Abati ta bayyana Ribadun da “karuwar siyasa kuma munafuki.”
Ribadu ya fadi a wurin wata lacca a Kaduna ranar Asabar da ta gabata cewa Najeriya a karkashin mulkin Jonathan, ta zama wadda ruwa ya ci, inda mugun mulki ya sanya aka yi watsi da bukatun al’ummar kasa.
Sai dai a martanin Fadar Shugaban kasa ta hannun Abati, ta nuna rashin jin dadi kan abin da ta kira munafunci da tsabagen karya da tozarta zababbiyar gwamnatin kasarsa da Ribadu ya yi domin son rai a kokarinsa na neman tagomashi a harkokin siyasar kasar nan bayan da ’yan Najeriya suka ki zabensa a zaben shekarar 2011.
Ya ce, “Idan Nuhu Ribadu na son yin magana kan zalunci, to ya yi kan lokacin da ya rika shirya tsige gwamnoni ta haramtacciyar hanyar amfani da ’yan majalisar da ba su kai adadin da ake bukata ba lokacin yaba jagorancin EFCC. Abin mamaki ne mutumin da ya tsara jerin sunan ’yan siyasa ya haramta musu tsayawa takara ba tare da umarnin wata kotu ko madogara ta shari’a ba, a ce yanzu har zai iya bugun kirji ya zargi mutumin da a karkashinsa aka gudanar da karbabben zabe a Najeriya ya ce masa jagoran “jirgin da ke neman nutsewa.” Akwai wani zaluncin da ya fi zaluncin tsige gwamnoni ko hana mutane tsayawa takara a dimokuradiyance ne?”
A martanin Ribadu, ta hannun kakakinsa Abdulaziz Abdulaziz, ya ce “Abin takaici ne yadda (Abati) ya amince da karairayin da ’yan siyasa da Malam Nuhu Ribadu ya hukunta suka kirkira, a kokarinsa na dafe wa mukaminsa.”
Kuma ya ce, babban tabargaza ce Abati ya zargi Ribadu da rashin godiya, domin Ribadu ne ya kamata ya yi irin wannan zargi na an ci amanarsa bayan ya sadaukar da kansa wajen yi wa kasarsa hidima a Kwamitin Cika-Aiki Kan Kudaden Shiga na Man Fetur. Abin tambaya shi ne wane ne ya kamata a tuhumi halinsa, wannan abu ne da ’yan Najeriya ya kamata su nemo amsarsa.”