Ribar banki da dangote ke samu za ta raba mutum miliyan biyu da talauci – Rahoto
Ribar banki (kudin ruwa) da attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka Alhaji Aliko dangote ke samu zai iya fitar da kimanin mutum miliyan biyu daga kuncin talauci. Wani bincike da kungiyar Bayar da Agaji mai suna Odfam ta bayyana haka a wani rahoto da ta fitar. kungiyar ta kuma ce tazarar da ke […]
Ribar banki (kudin ruwa) da attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka Alhaji Aliko dangote ke samu zai iya fitar da kimanin mutum miliyan biyu daga kuncin talauci.
Wani bincike da kungiyar Bayar da Agaji mai suna Odfam ta bayyana haka a wani rahoto da ta fitar.
kungiyar ta kuma ce tazarar da ke tsakanin talakawa da attajirai ta karu a bana, kamar yadda gidan rediyon BBC ya ruwaito a shekaranjiya Laraba.
kungiyar wadda take a Birtaniya ta ce biloniyoyi 42 da suke sassan duniya sun samu Dala biliyan 3 da miliyan 600, kuma kashi daya cikin 100 na attajiran duniya ne suke tafiyar kashi 82 cikin 100 na dukiyar da ke fadin duniyar.
kungiyar Odfam ta ce abin da ya kara taimaka wa manyan attajiran wajen tara dimbin dukiya shi ne yadda wadansu daga cikinsu suke kauce wa biyan haraji da kuma yadda suke amfani da gwamnatoci wajen yin dokoki da za su ci gajiyarsu.
Sai dai masana a fannin hada-hadar kudi sun sanya alamar tambaya game da wasu daga cikin abubuwan da kungiyar take ikirari.
Manyan attajirai shida da suka fi kudi a duniya su ne:
1. Jeff Bezos Dala biliyan 110.7 (Amurka)
2. Warren Buffett Dala biliyan 92.6 (Amurka)
3. Bill Gates Dala biliyan 92.6 (Amurka)
4. Amancio Ortega Dala biliyan76.4 (Spain)
5. Mark Zuckerberg Dala biliyan 74.7 (Amurka)
6. Carlos Slim Helu Dala biliyan 69.8 (Meziko)
Shugaban kungiyar Odfam Mark Goldring ya ce wannan rahoton ba labari ne mai dadi ba ga duniya.
Rahoton yana zuwa ne a daidai lokacin da aka fara wani babban taro tattalin arziki na duniya a birnin Dabos na kasar Switzerland.
Manyan ’yan kasuwa suna halartar taron ne duk shekara don tattauna hanyoyin da za su yi amfani da dukiyarsu wajen taimakon sauran mutane mabukata.