Rigakafin kamuwa da MMM

Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.Ga bayani kan hanyoyin da matasan da ba su riga sun yi aure ba za su yi wa kansu rigakafin kamuwa da matasalar matasan magidanta, (MMM) da fatan Allah Ya […]

Rigakafin kamuwa da MMM
Rigakafin kamuwa da MMM

Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Ga bayani kan hanyoyin da matasan da ba su riga sun yi aure ba za su yi wa kansu rigakafin kamuwa da matasalar matasan magidanta, (MMM) da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
•       Ga Matasan da ba su yi aure ba, da wadanda suke cikin farkon balagarsu, yana da matukar alfanu su yi wa kansu rigakafin faruwar wannan matsala gare su nan gaba idan sun yi aure. Kamar yadda ya gabata a bayananmu na baya, kusan kashi 90 na masu fama da wannan matsalar sun kamu da ita ne a dalilin tsananin sabo da yin zinar hannu lokacin samartakarsu.
•       Annanbinmu SAW ya ba mu cikakke kuma ingantaccen maganin tsananin sha’awa: shi ne yin azumi a-kai-a-kai, baya ga maganin tsananin sha’awa, ga ladar da mutum zai samu ta yin azumi da kuma ta bin umarnin Manzon Allah SAW, sannan ga karin imani da takawa da son Allah da kara tsayar da addini, to don me matasa ba za su rika yin wannan ba sai su biye wa shaidan su rika aikata sabo da kawunansu, sabon da zai haifar musu da matsaloli daban-daban ba ma kawai na fitar maniyyi da wuri ba?
•       Iyayen wannan lokaci suna sakaci sosai da matasan ‘ya’yansu, sai a bar zabga-zabgan matasa suna zaman banza ba su aikin komai, sai kalle-kallen fina-finai da sauraren kade-kade da wake-wake, wadanda duk tamburan shaidan ne masu kara kusanto shaidan ga dan Adam. Kamata ya yi da yaro ya tasa a samar masa wata ‘yar sana’a da zai rika yi bayan makaranta, kada a saba masa da zama haka nan ba yin komai, wannan shi ke sa kuzarin sha’awa ya taru ya yi yawa a jikinsa har ya kai shi ga aikata zinar hannu. Amma in kullum yana cikin sha’anoni daban-daban, ga karatun Islamiyya da na haddar kur’ani Mai Girma, ga sana’o’in hannu yana koyo, yau wannan; gobe wani abu daban, a koya masa sada zumunci, ayyukan sadaukarwa don taimakon al’umma, noma, da sauran duk ayyuka na alheri wadanda gara ya yi amfani da kuzarinsa wajen yinsu da a ce ya zubar da shi a banza wajen yin zinar hannu ko wani aikin alfasha. Da wuya ka ji wannan matsalar na faruwa a cikin matasa kauyawa, saboda su kullum cikin aikin karfi suke kuma ba su yawan kallace-kallacen abubuwan da ke takulo sha’awa, sannan da wuya saurayi ya kai shekara ashirin ba a yi masa aure ba. Da fatan Allah Ya taimake mu Ya ba mu iko da karfin halin inganta da kyautata halayyar mu da ta ’ya’yanmu kodayaushe, amin.
Amsoshin Tambayoyinku
Ko MMM na hana haihuwa?
Shin ko matsalar fitar maniyyi da wuri na hana haihuwa? Domin ina fama da wannan matsala ga shi har yanzu uwargidana ba ta samu juna biyu ba bayan shekara uku da aure.
Amsa
Fitar maniyyi da wuri na iya hana haihuwa; domin wasu abin yakan zo musu da wuri sosai tun kafin su kasance cikin ainihin yanayin gabatarwar ibadar aure ko kuma kafin su karasa daidaita. To, a irin maniyyi ba zai samu isa ga mahaifa ba balle har a samu haduwar kwan mace da na namiji da zai samar da daukar ciki ga macen. Bayan matsalar fitar maniyyi da wauri, akwai wasu matsalolin da ka iya hana isar maniyyi ga mahaifa, don haka ya fi kyau a ga likita a yi masa bayani don gane ainihin inda matsalar take.
Bambanci tsakanin maniyyi, maziyyi da wadiyyi.
Dan Allah ina so ku yi mana bayanin bambanci tsakanin maniyyi, maziyyi da wadiyyi; da yadda za a iya bambance su in sun bayyana.
—Ummi Kano
Amsa
1.  Maniyyin da namiji wani farin ruwa ne mai kauri, danyensa yana kamshi irin na furen dabino, in ya bushe kuma yana karni irin na kwai. Na ‘ya mace kuma ruwa ne launin ruwan dorawa kuma marar kauri. Duk suna fita lokacin da aka cim ma biyan bukatar sha’awa; kamar Yadda Manzon Allah SAW ya bayyana a cikin Hadisin da aka karbo daga Umm Sulaym RA.
2.    Maziyyi kuwa ruwa ne mai kauri kuma mai garau-garau; yana fita ne lokacin da jin motsuwar sha’awa ya game jiki, amfaninsa ga maza shi ne fitar da ragowar fitsari daga kwararon hanyar da maniyyi zai fita, don kada ya lahanta kwayayen halittar da namiji kafin su isa ga mahaifa; haka kuma suna bayar da kariya ga al’aurar namiji daga wasu sinadarai na al’aurar ‘ya mace. A jikin ‘ya mace kuma amfanin shi ne bayar da isasshiyar lemar da za ta haifar da saukin gabatarwar ibadar aure.
3.    Wadiyyi kuwa wani farin ruwa ne, curarre kuma mai kauri, yana yanayi da maniyyi, sai dai ya fi maniyyi curewa; yakan fita kafin ko bayan yin fitsari sai dai ya fi yawan fita bayan yin fitsari.
4.    Maniyyin da  ya fita dalilin ibadar aure, zinar hannu ko dalilin mafarki dole sai an yi wankan tsarki kafin a ci gaba da ibada; amma wanda ya fita dalilin aikin karfi ko tsananin wahala to ba sai an yi wankan tsarki ba, sai dai a yi tsarki, a ci gaba da ibada.
5.    Maziyyi da wadiyyi ba a yi masu wankan tsarki, sai a yi tsarki tare da wanken wajen da suka taba a jiki ko tufafi.
6.    Maziyyi da wadiyya najasa ne don haka tufar da suka taba ba za a iya Sallah da ita sai an tsarkaketa da ruwa mai tsarki. Amma maniyyi, ana iya yin gogewa kawai in danye ne ko a kankare shi in ya riga ya bushe.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba in Allah SWT Ya kaimu. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.