Rigimar bikin haihuwa ta yi ajalin mutum biyu a Abuja
Wadansu matasa da aka bayyana a matsayin ’yan kungiyar asiri da suke hamayya da juna, sun kara a tsakaninsu inda lamarin ya kai ga ajalin mutum biyu, daya daga cikin kowane bangare. Lamarin wanda ya faru a ranar Lahadin da ta gabata da dare a garin Karmo da ke Abuja, Aminiya ta samu labarin cewa […]
Wadansu matasa da aka bayyana a matsayin ’yan kungiyar asiri da suke hamayya da juna, sun kara a tsakaninsu inda lamarin ya kai ga ajalin mutum biyu, daya daga cikin kowane bangare.
Lamarin wanda ya faru a ranar Lahadin da ta gabata da dare a garin Karmo da ke Abuja, Aminiya ta samu labarin cewa matsalar ta faro ne a yayin bikin murnar ranar haihuwar wani matashi daga cikin kungiyoyin asirin biyu masu suna ‘Black Ade’ da kuma ‘Arrow Bagger’ lamarin da ya kai ga watsewa ba shiri daga bikin.
Wakilinmu wanda ya ziyarci yankin a ranar Talatar da ta gabata, ya samu labarin cewa da farko wani matashi mai suna Haruna Aminu wanda ke da zama a Unguwar Hausawa a Karmo aka auka masa a wajen taron, inda aka garzaya da shi zuwa babban asibitin gwamnati da ke Gwarinpa, kafin a wuce da shi zuwa Asibitin Kasa na Abuja, inda ya cika a ranar Litinin.
Bayanai sun ce tun a daren da aka yi hatsaniyar ce mambobin bangaren matashin suka kai harin daukar fansa a kan wani matashi mai suna Yusuf Ismaila a gidansu da ke Unguwar Gade da ke garin, inda aka kashe shi nan take.
Wadansu da lamarin ya faru a gabansu sun bayyana cewa wadansu matasa da ke da alaka da bangaren wanda aka kashe daga baya, sun jawo takaddama lokacin da ake shirin yi masa jana’iza a ranar Litinin, inda suka hana a binne gawarsa bayan an yi mata sutura.
Sai dai a cewar majiyarmu matasan sun janye daga bisani zuwa wata gonar kashu da ke kusa da unguwar, bayan wadansu manya sun shawo kansu, inda aka binne shi. Daga baya ne kuma suka sake tayar da bore ta hanyar zanga-zanga, sai da ’yan sanda tare da gudunmawar ’yan kungiyar sintiri sun samu nasarar wargaza su.
Haka nan ’yan bangan sun rusa wasu dakuna biyu da aka bayyana a matsayin dakin jagoran daya daga cikin kungiyoyin asirin biyu mai suna Johnson da ke da lakabin J. Blank da kuma wansa a gidan iyayensu da ke Unguwar Idu Gbagyi a garin.
Wani jagoran ’yan banga da ya zagaya da wakilinmu a gidan, ya ce daukar matakin ya biyo bayan tserewar matashin ne tare da iyayensa, duk da gayyatarsu da jami’an tsaro suka yi bayan aukuwar matsalar.
Babban Jami’in ’Yan sandan Karmo, CSP Ahmed Alhassan wanda ya tabbatar da faruwan lamarin, ya ce tuni aka kama mutum biyar da ake zargi da hannu a lamarin.
A ranar Talatar da ta gabata ce kuma aka samu nasarar karbo gawar daya wanda ya cika a asibitin, inda bayanai suka ce an bukaci makudan kudi a matsayin na ajiyar gawar, sannan kuma jama’a suka kaurace wa jana’izarsa bayan samun labarin abin da aka danganta da mamacin.