Rigimar Taraba ta fara lafawa

Rigimar siyasa da ta taso a Jihar Taraba sakamakon dawowar Gwamnan Jihar danfulani danbaba Suntai da ke fama da rashin lafiya bayan ya shafe wata 10 yana jinya a kasar waje ta fara lafawa, bayan da shugabannin Jam’iyyar PDP na kasa suka shiga tsakani.Wani kwamitin jam’iyyar a karkashin Sanata Hope Uzodinma da suka je jihar […]

Rigimar Taraba ta fara lafawa

Rigimar siyasa da ta taso a Jihar Taraba sakamakon dawowar Gwamnan Jihar danfulani danbaba Suntai da ke fama da rashin lafiya bayan ya shafe wata 10 yana jinya a kasar waje ta fara lafawa, bayan da shugabannin Jam’iyyar PDP na kasa suka shiga tsakani.
Wani kwamitin jam’iyyar a karkashin Sanata Hope Uzodinma da suka je jihar a ranar Litinin da ta gabata ne ya bayyana haka, bayan ganawa a asirce da masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati da ke Jalingo.
Sanata Uzodinma ya shaida wa manema labarai cewa Alhaji Garba Umar zai ci gaba da kasancewa mukaddashin Gwamna yayin da Suntai zai ci gaba da jinya har zuwa farfadowarsa.
 Ya ce,“Mun warware matsalar, dama rashin fahimta ce ta tsakanin iyali; ba mu da wani rikici a Taraba. Gwamna shi ne Suntai, kuma yana samun lafiya, babu wata rigima tsakaninsa da mataimakinsa wanda yanzu shi ne Mukaddashin Gwamna.”
Ya ce, Suntai “Yana goyon bayan Mukaddashin Gwamnan ya ci gaba da riko, kuma kowane lokaci zai rika tuntubarsa kan muhimman al’amura har zuwa lokacin da zai iya karbar harkokin mulkin jihar kamar yadda aka cimma matsaya a tsakanin dukkan bangarorin.”
Da yake bayani ga manema labarai bayan ganawar Mukaddashin Gwamna Umar ya ce an warware sabanin kuma an amince ya ci gaba da jagorancin al’amuran jihar har zuwa lokacin da Suntai zai iya komawa kan aiki a matsayin Gwamna.
“Ina son tabbatar muku a yau cewa, mun gaya wa juna gaskiya, kuma mun warware sabaninmu. Ina tabbatar muku cewa Taraba daya ce. Dukkanmu mun rika ganin yadda jaridu a tsawon mako suka rika rubuta labarai iri-iri kan Taraba. To yau mun gode Allah mun warware dukkan sabaninmu kuma an amince in jagoranci harkokin jihar har zuwa lokacin da maigidana zai iya dawowa ya fara aiki a matsayin gwamnanmu.”  
Game da rushe Majalisar Zartarwar Jihar, ya ce yana tatttaunawa da maigidansa kan yadda za a kafa sabuwar majalisa.
Kwamitin na Uzodinma da Mukaddashin Gwamnan da wakilan majalisar tarayya daga jihar da na majalisar jihar sun kai ziyarar girmamawa ga Suntai a gidan gwamnati kafin ganawar.
Kuma masu daukar hoto na gidan talabijin na Taraba da na Channels da na Tb Continental da kuma wani dan jarida daga Daily Newswatch kadai jami’an tsaro suka bari suka halarci ganawar kwamiin da Suntai, yayin da aka hana sauran manema labarai.
An ce Suntai ya yi musabaha da wakilan kwamitin, a lokacin ganawar da matarsa Hauwa Suntai da shugaban majalisar Taraba da manyan ’ya’yan PDP na Taraba suka halarta.