Rigingimu sun taso a takarar sarautar Sarkin Hausawan Abuja

Sama da shekara daya bayan rasuwar Sarkin Hausawan Abuja Alhaji Ahmad Girema, zaben sabon sarki da zai maye gurbinsa na neman ya gagari al’ummar Hausawan da Shugaban Majalisar Sarakunan Birnin Tarayya kuma Ona na Abaji Alhaji Adamu Yunusa, wanda ke nada sarkin da Hausawa suka zaba.Aminiya ta samu labarin cewa takaddamar ta faro ne bayan […]

Rigingimu sun taso a takarar sarautar Sarkin Hausawan Abuja

Yan takaraSama da shekara daya bayan rasuwar Sarkin Hausawan Abuja Alhaji Ahmad Girema, zaben sabon sarki da zai maye gurbinsa na neman ya gagari al’ummar Hausawan da Shugaban Majalisar Sarakunan Birnin Tarayya kuma Ona na Abaji Alhaji Adamu Yunusa, wanda ke nada sarkin da Hausawa suka zaba.
Aminiya ta samu labarin cewa takaddamar ta faro ne bayan sadakar uku na tsohon Sarkin Hausawa Girema, wanda ya rasu a ranar 28 ga watan Fabrairun bara, lokacin da sarakuna 13 na Hausawan yankin Birnin Tarayya suka yi zama a gidansa wanda shi ne babbar fadar Hausawan birnin, don zaben sabon sarkin, sai wasu aminansa da ya ba su sarautu a fada suka sanar da sarakunan cewa, akwai tsari da ya bari, ya kuma nada masu zaben sarki, saboda haka aka dakatar da zaman, inda suka sanar da sarakunan cewa sai wanda sunansa ya fito daga cikin mutum bakwai ne kawai da kundin da ya bari ya nuna, ke da hurumin zama don zaben sabon sarkin.
Wannan al’amari a cewar majiyar Aminiya, ya jawo jayayya a tsakanin sarakunan 13 da kuma mutum bakwaid a kundin da a ka ce marigayin ya bari ya nuna, al’amarin da ya sa har yanzu Hausawa ba su da Sarki a birnin kamar takororinsu Yarabawa da Ibo, wadanda bayanai suka ce sun zabi sarakunan ne a birnin, a matsayin koyi da Hausawa, bayan marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha ya tabbatar wa marigayi Grema sarautar Sarkin Hauswa na farko, ta hannun Ministan Abuja na lokacin Janar Jeremiah Usene.
Sarkin Hausawan Gwagwalada Alhaji Sani Abubakar, wanda ke matsayin shugaban sarakunan Hausawa 13 na Abuja a halin yanzu, da suka hada da na: Garki da Karu da Karshi da Jiwa da Bwari da Zuba da Kwali da Rubochi da Kuje da Gwargwada da Yaba da kuma Abaji da suka zabe shi a matsayin jagoran riko kafin zaban sabon Sarkin, ya bayyana wa Aminiya cewa su ne ke shugabantar Hausawan Abuja a matakan garuruwa, kuma su ne suka cancanci zaba wa al’ummar jagora da zai jagorance su a sarauta. Sarkin Hausawan ya ce shi da sauran sarakuna 12 ba su yarda da kundin ba, bare abin da ke cikinsa, saboda ba a tuntubesu ba a lokacin da a ka tsara shi, kuma ba su tashi saninsa ba sai bayan rasuwar Sarki Girema..
Ya ce tsarin da aka bi wajen nada sarki Girema an yi shi ne a lokacin soja, kuma amfani da shi a halin yanzu zai yi wuya. Ya yi zargin cewa mutum bakwai da kundin ya nuna za su yi zaben, aminai ne da abokan hulda na marigayi Sarkin, wadanda akasarinsu ya dauko su ne daga Legas bayan ya samu sarautar, kuma ba yadda wadanda suka same su a Abuja shekara da shekaru za su zaba musu jagora, alhali ba sa wakiltar kowa, a maimakon su da ke tare da jama’ar masarautun Hausawa 13 na Abuja.
A ganawarsa da Aminiya, daya daga cikin ’ya’yan marigayi Sarkin Hausawa Abba Hassan Girema, ya tabbatar da bayanin jagoran sarakuna 13 da kuma mum bakwai  da kundin da a ke cece-kuce ya nuna a matsayin babbar takaddamar, sai dai ya ce daga cikin mutum bakwai da kundin ya nuna za su yi zaben akwai wasu daga cikin sarakunan Hausawan 13. Ya ce su a bangarensu na ’ya’yan marigayin sun yi ittifaki sun zabi Alhaji Assil Ahmad Girema a matsayin dan takararsu, kasancewar shi ne ya rika tallafa wa mahaifinsu a harkar sarauta, kuma a shirye suke a bi duk hanyar da za ta kawo ci gaba da zaman lumana wajen zaben sabon Sarkin.
 Sarkin Hausawan Garki Alhaji Umar Abubakar Abdullahi, daya daga cikin sarakuna 13 da ke ikirarin su ne kadai suka cancanci yin zaben, kuma sunansa ya fito a cikin mutum  bakwai da kundin ya ce su ne kadai ke da hurumin zaben Sarkin Hausawan Abuja, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Ni kaina ban tashi sanin ina cikin mutum bakwai din ba, sai bayan rasuwar Sarki Girema, lokacin da muka yi zaman farko da takwarorina 12, a lokacin ne mukarrabansa suka dauko wannan takarda daga ma’ajiyarsa, suka ba ni takardar shaidar kasancewa mamba a ciki, sai dai wannan kundi ni a ganina ya saba doka, don an tsara shi ne ba tare da yawu ko masaniyar sauran sarakuna ba.
Da wakilinmu ya garzaya babban ofishin da ke kula da al’amuran sarautu da kananan hukumomi na Birnin Tarayya, Sakataren Sashin Barista Yahaya Alhasan Gwagwa, ya tabbatar da cewa bayan takaddamar, sashinsa ya yanke shawarar, zai tuntubi sarakunan 13 su hada kai da mutum bakwai din wadanda akwai wasu daga cikinsu don gudanar da zaben sabon Sarkin tare.  Ya ce an shirya yin zaben ne bayan Sallar Azumi.
Zuwa yanzu dai, akwai mutum hudu da ke neman sarautar da suka hada da: Alhaji Assil Ahmad Girema dan marigayi Sarkin Hausawan da Madakin Sarkin Hausawan Karu Alhaji Isma’ila Musa da Sarkin Hausawan Jiwa Alhaji Bello Sa’idu, sai kuma Madawakin Anka, wanda ba mu samu suna da hotonsa ba.
Yunkurin zaben sau uku a baya ya ci tura, na baya-baya da aka shirya yi a fadar Ona na Abaji, ofishin masarautu na Abuja ya dakatar da shi, bisa zargin ba a sanar da hukuma ba kamar yadda majiyoyi da dama suka tabbatar wa Aminiya.