Rigirmar manoma da makiyaya a Nasarawa da Benuwai kabilanci ne – Babban Sufeton ‘Yan Sanda
Babban Sufeton ‘Yan Sanda na kasa, Ibrahim Idris ya nanata cewa rigingimun da suka ki ci suka ki cinyewa tsakanin manoma da fulani makiyaya da ke iyakokin jihohin Benuwai da Nasarawa na kabilanci ne. Ya bayyana haka ne a wajen wani taron zaman lafiya na masu ruwa da tsaki daga Jihar Nasarawa da Benuwai da […]
Babban Sufeton ‘Yan Sanda na kasa, Ibrahim Idris ya nanata cewa rigingimun da suka ki ci suka ki cinyewa tsakanin manoma da fulani makiyaya da ke iyakokin jihohin Benuwai da Nasarawa na kabilanci ne. Ya bayyana haka ne a wajen wani taron zaman lafiya na masu ruwa da tsaki daga Jihar Nasarawa da Benuwai da aka gudanar a Lafia fadar gwamnatin Jihar Nasarawa, don kawo karshen rigingimu da kashe-kashe da ke cigaba da aukuwa tsakanin al’ummomin da ke iyakokin jihohin biyu.
Ya bayyana cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya umurce shi da ya kasance a Jihar Benuwai da Nasarawa ne don neman hanyoyin magance matsalolin. Yana mai cewa, “Har yanzu ina kan bakana cewa rigingimu da ke faruwa tsakanin al’ummar fulani makiyaya da manoma ‘yan kabilar Tibi da ke iyakokin jihohin Nasarawa da Benuwai ba komai ba ne face kabilanci, domin bincike da rahotanni da nake samu kawo yanzu sun tabbatar da haka.
“Shi ya sa da na zo banyi wata-wata ba na gayyaci wasu daga cikin manyan kabilun wadannan jihohi, musamman al’ummomin fulani da takwarorinsu Tibi manoma don mu tattauna yadda za mu shawo kan matsalar. Domin ta haka ne kawai na tabbata za a iya magancewa ko rage rigirgimun. Wadannan mutane ne da suka zauna lafiya da junansu da dadewa kuma ya kamata ace sun kasance ‘yan uwan junansu. Ya kamata kowa ya rika hakuri da dan uwansa, kasancewar dukanmu ‘yan Najeriya ne.
A gaskiya babu wata ko wani dake da iko ya hana wata ko wani dan Najeriya zama a duk inda ya ga dama, shi yasa ya zame mana dole mu rika hakuri da juna kuma mu dauke batun hakurin da muhimmanci. Na kasance kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Nasarawan nan kuma na fuskanci abin da kuke fuskanta tsakaninku biyu a yanzu a lokacina, shi yasa nake kara nanata cewa rigimar na kabilanci ne. Saboda haka dole mu nemi hanyoyin maido da zaman lafiya a wadannan wurare” Daga nan sai ya bukaci wadanda ke fada da junansu da sauran ‘yan Najeriya baki daya a duk inda suka sami kansu da su yi kokari su zauna lafiya da junansu don a samu dawwamammen zaman lafiya a jihohin da kasa baki daya.
Shi kuma da yake jawabi dangane da hare-hare da a cewarsa wasu fulani makiyaya ke kai wa al’ummar Tibi dake wasu kauyuka a Jihar Benuwai da wadanda ke iyakokin jihar da Nasarawa, shugaban al’ummar Tibi dake jihar Nasarawa, Barrista Gabriel Akaaka ya shaida wa babban sufeton na ‘yan sanda cewa al’ummar Tibi da dama ‘yan asalin Jihar Nasarawa, sun rasa rayukansu da dukiyoyinsu da dama sakamakon dokar hana kiyo a fili da gwamnatin jihar Benuwai da majalisar dokokin jihar suka kafa a kwanan nan.
Ya ce ya tabbata cewa babban abin da zai kawo karshen rigingimu da kashe-kashen shi ne a rika bayyana inda wadannan masu kisa suke boyewa suna aikata munanan ayyukansu, kuma a cewarsa ya tabbata hukumomin tsaro dake jihohin da na kasa tare da hadin kan shugabannin al’ummomin za su iya yin haka. Barrista Akaaka wanda shi ne kuma kwamishinan muhalli da raya albarkatun kasa na Jihar Nasarawa, ya kuma bayyana a taron cewa wadannan hare-hare da ake kai wa al’ummarsa Tibi ba ainihin fulani ‘yan jihar ne ke yi ba, inda ya ce wadanda ke bi ta jihar ne zuwa wasu johohi daban ke aikata ta’asar, sannan ya bukaci al’ummomin wadannna kauyuka ko garuruwa da suke bi su rika sanar da hukumomi da suka dace a duk lokacin da suka ga bakin fulani makiyaya ko wani daban a yankunan nasu kuma ba su yarda da ayyukansa ba.
Daga nan ya ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro tare da hadin kan al’ummomin jihohin biyu baki daya za su hada kai don magance lamarin kwata-kwata. A nasa bangaren, Mai Martaba Sarkin Tunga, Alhaji Bala Galadima a jihar Nasarawa, inda ake zargi cewa fulani dake aikata ayyukan ta’asar suna boye a garinsa ne, sannan kuma daga wurin suke kai hare-hare kan wadannan kauyuka har da Jihar Benuwai, ya yi amfani da damar ya musanta zargin, inda ya bayyana cewa al’ummar Tibi manoma da takwarorinsu fulani makiyaya sun dade suna zaman lafiya da junansu a yankin, ba su taba fuskantar wani rashin jituwa da ya kai ga kashe-kashe ba, kafin daga bayannan da gwamnatin Benuwai ta kirkiro da wannan dokar hana kiwo a fili. Ya cigaba da bayyana cewa
“A gaskiya ina so in yi amfani da damar nan in bayyana rashin jin dadina da masarauta da al’ummar Tunga baki daya dangane da jita-jita da wasu a jihar nan da Benuwai har da shi kansa gwamnan Jihar Benuwai, Sam Ortom suke yadawa cewa ana boye fulani dake kai hare-hare a kauyuka da garuruwa dake iyakokin jihohin biyu musamman Benuwai a garinmu Tunga. Hakan ba gaskiya ba ne. Kuma kowa musamman gwamnatin Jihar Nasarawa za ta iya tabbatar da cewa sau da yawa babu wadanda suke taimaka mata da hanyoyin magance bala’in kamar al’ummar Tunga.
Daga nan ya bukaci al’ummomi da gwamatotin jihohin biyu dama gwamnatin tarayya su yi wasi da zargin, don a cewarsa ba su da tushe balle makama. Haka su ma da aka ba su dama su kare kansu daga zargin shugabannin fulani da Tibi dake yankin na Tunga, Ardo Maishanu da Mista Zaki Gaso duk sun bayyana cewa babu wani ko wata da ta bukaci Tibabe su bar yankin sakamakon rigingimun, inda suka kuma bayyana cewa babu wani fulani ko wasunsu dake tada zaune-tsaye a yankin kuma ba sa boye kowa dake da mummmun nufi a yankin baki daya. Su ma sun yi kira a yi wasi da zargin, inda sun kuma bukaci gwamnatotin jihohin biyu da na tarayya su inganta harkokin tsaron a yankin.
Shi ma a jawabinsa, shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders na Jihar Nasarawa, Alhaji Husseini Mohammed ya ce kungiyar ba ta san wadanda ke kai hare-haren ba, kuma tana yin duk iya kokarinta wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin mambobinta da takwarorinsu Tibabe manoma da sauran al’ummar duka jihohin biyu. Ya bukaci gwamnatin tarayya ta samar da hanyoyin magance rigingimun musamman samar wa falani da wajen kiwo da sauransu ta kuma yi la’akari da munanan sakamako da dokar hana kiwo a fili da gwamnatin Benuwai ta kafa don a cewarsa hakan ba shakka yana rura wutar rigingimun ne ba haifar da alheri ba.