Rika Okada, wadda aka aike da gawarta ta gidan waya aka rubuta ’yartsana
Masu yawon bude ido daga sassa da dama na duniya na ziyartar wuraren shakatawa da ke kasar Philipines da Isra’ila don a yi musu tausa da macizai.Wuraren shakatawar da ake yin tausa da macizai sun hada da gidan kiwon namun daji na birnin da ake kira Cebu City Zoo da ke kasar Philipines da kuma […]
Masu yawon bude ido daga sassa da dama na duniya na ziyartar wuraren shakatawa da ke kasar Philipines da Isra’ila don a yi musu tausa da macizai.
Wuraren shakatawar da ake yin tausa da macizai sun hada da gidan kiwon namun daji na birnin da ake kira Cebu City Zoo da ke kasar Philipines da kuma wani wurin shakatawa da ake kira Ada Barak’s Spa da ke Arewacin kasar Isra’ila.
Jami’ar da ke kula da wurin shakatawa na Ada Baraka da ke kasar Isra’ila mai suna Barak ta shaidawa kafar yada labarai ta Yahoo News cewa mutane suna sha’awar abin.
Ta ce ‘Saboda sha’awar da mutane suke da ita na yin tausa da macizai za ka ga suna tururuwa daga kasashe da dama suna zuwa. Kuma kullum muna samun karuwar sababbabin abokan hulda’.
Ta ci gaba da cewa ‘A dalar Amurka 80 kawai macizai daban-daban za su yi yawo a jikinka su yi maka tausar da ba a taba yi maka irinta ba. Su bi dukkan sassan jikinka har da fuska su kawar da duk wata gajiya da ciwo na jikinka ba tare da wata matsala ba. Ba wani hadari kuma ba wani cutarwa, macizan ba za su yi maka komai ba saboda mun dauki dukkan matakan da suka kamata wajen ganin cewa macizan ba su cutar da mutum ba’.
Shi ma manajan wurin kallon namun daji na birnin Cebu da ke Philipines Giobanni Romarate ya ce ‘Da farko masu ziyara suna tsorata amma wadanda suka gwada yin tausa da macizan suna sha’awar a sake yi musu saboda ya fi taussa da hannu’.
Ya bayyana cewa macizan masu suna Michelle da Walter da EJ da kuma Daniel ba sa cutarwa sannan kuma suna daukar kimanin mintina 15 suna yi wa mutum tausa.
Ya kara da cewa sai dai macizan ba su son mutum ya fiya yawan numfashi da karfi ko yawan motsi ko kuma ya hura musu iska don sai su dauka mutumin zai cutar da su ko kuma abincin su ne.