Rikici a kan tabar wiwi ya yi ajalin mutum daya a Gombe
Kwastomomi sun kashe dilan tabar wiwi a rikicin da ya barke tsakaninsu kan tabar wiwinsa a Gombe.
Ana cafke wasu matasa uku sun kashe wani dilan tabar wiwi saboda sabanin da ya shiga tsakaninsu da shi kan tabar wiwi a Jihar Gombe.
Rundunar ’yan sandan jihar ta kama matasan ne a Unguwar Gabas da ke garin Deba na Karamar Hukumar Yamaltu, bayan sun yi wa dilan wiwin wannan aika-aikan.
Kakakin rundunar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar ya shaida wa manema labarai a yayin da yake holen maatasan cewa a ranar 12 ga watan Fabarairu 2024 wani mai suna Mustapha Mato ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na garin Deba da cewa fada ya kaure a tsakanin wadannan matasa uku da wani dan shekara 30 da suka caka wa wuka ya mutu.
A cewarsa, suna samun wannan rahoto ne jami’ansu suku bazama domin gudanar da bincike, inda suka gano cewa wanda aka kashe din dilan tabar wiwi ne kuma rikici tsakanin sa da kwastomominsa ne ya jawo fada har suka soke shi da wuka ya ce ga garinku nan.
Ya ce, ’yan sandan na ci gaba da gudanar da binciken kan wadanda aka kama kuma da zarar sun kammala za su tura su zuwa kotu.
Aminiya ta zanta da matasan uku wadanda suka labarta mata yadda lamarin ya kasance har ta kai ga mutuwar abokin fadan nasu, inda suka ce fada ne ya hada su bayan ’yan sanda sun kai masa samame ya gudu ya bar tabar wiwinsa.
Matasan da ke hannu sun ce bayan faruwar hakan ce washegari ya yi zargin cewa su ne suka kwashe masa tabar wiwinsa da ya tsere ya bari.
Sun ce, a dalilin haka ne ya tattaro yara da adduna da wukake inda a garin fada suka soki daya daga cikinsu, sai su ma suka kwace wukar suka caka wa Sama’ila a baya da kuma wuyansa, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.