… Rikici a PDP ba sabon lamari ba ne – Lamido
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce rikicin da Jam’iyyar PDP ke fuskanta ba wani abin daga hankali ba ne, domin rikici a cikin jam’iyyar siyasa ba sabon lamari ba ne. Alhaji Sule Lamido ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a gidansa da ke Bamaina a kusa […]
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce rikicin da Jam’iyyar PDP ke fuskanta ba wani abin daga hankali ba ne, domin rikici a cikin jam’iyyar siyasa ba sabon lamari ba ne.
Alhaji Sule Lamido ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a gidansa da ke Bamaina a kusa da Dutse fadar jihar, inda ya ce rikici a tafiyar Jam’iyyar PDP shi ne gishirinta, kuma ba abu ne da zai tarwatsa ta ba, domin jam’iyyar ta fada cikin rigima iri-iri a baya amma an wayigari tana nan daram.
Alhaji Sule Lamido ya ce da rigima za ta tarwatsa jam’iyyar da ta tarwatse tun a zamanin rigimar su Audu Ogbe, “kuma batun cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar yana goyan bayan bangaren Sanata Ahmed Makarfi ko kungiyar ACF tana mara wa bangaren Sanata Ali Modu Sheriff duk maganganu ne marasa kan gado, mun san matsalarmu, za mu daidaita kanmu,” inji shi.
Ya ce duk ’ya’yan PDP da suka bar ta da wadanda suke cikinta kansu a hade yake, kuma wadanda suka tafi in suka dawo gidansu sallama kawai za su yi su shige domin dama ’ya’yan gidan ne kuma uwarsu tana nan a ciki.
Alhaji Sule Lamido ya nuna takaici game da yadda gwamnatin Jam’iyyar APC ke danganta ’ya’yan Jam’iyyar PDP da cewa masu zunubi ne, yayin da take nuna ’ya’yan Jam’iyyar APC da cewa su waliyai ne komai suka yi ba laifi ba ne. “Hakan ba adalci ba ne, idan haka ne kada Shugaba Buhari ya manta wadancan da ake cewa masu zunubi ne su ne suka fito daga gidan zunubi suka mara masa baya ya kafa gwamnati ke nan masu zunubi ne suka haifi ’ya mai zunubi wato APC,” inji Lamido.
Da ya juya kan rikicin yankin Neja-Delta da wasu tsageru ke haddasawa yi, ya ce rashin adalci na wasu shugabannin kasar nan a shekara 30 baya ya jawo haka, “Rikicin Neja-Delta rikici ne da ya shafi kowa a Najeriya ba rikici ne da za a rika zargin wadansu tsirari ne suke rura wutarsa ba, kuma bai kamata a zargin wasu gwamnoni ko ’ya’yan PDP da rura shi ba.