Rikici: An jikkata mutum biyu saboda awarar Naira 300 a Kano
Rundunar ’yan sandan Kano ta ce ta cafke kusan mutum 30 da ake zargin hannunsu a rikicin.
Mutum biyu sun jikkata sakamakon wani rikici da ya barke saboda awarar Naira 300 a tsakanin Fulanin garin Keba da Hausawan garin Tukwi a Karamar Hukumar Makoda da ke Jihar Kano.
Aminiya ta ruwaito cewa, rikicin ya barke ne a daidai lokacin da wani mutum mai suna Nasiru Abdullahi wanda aka fi sani da Dan Sanda ya sayi awarar Naira 300 a wurin wata yarinya da ke sayar da awarar, inda aka rasa canjin Naira 500.
- Kotun Daukaka Kara ba ta yi min adalci ba — Gwamnan Filato
- Dan daba ya kashe limami saboda hana shi shan wiwi a Kano
Hamisu Idris wani wanda abin ya faru a kan idonsa, ya bayyana cewa bayan mutumin ya sayi awarar ce ya bai wa yarinyar Naira 500 amma saboda ta ce ba ta da canji sai ya kwada mata mari.
“Bayan shi wannan da ake ce masa Dan Sanda ya sayi awara sai ya ba ta Naira 500 don ta dauki kudinta Naira 300, amma sai ta ce ba ta da canji.
“Shi kuma sai ya ce sai ta ba shi kudinsa. Ita kuma saboda tsoron kada ya gudu da kuɗinta sai ta ki bayarwa ta ce za ta je ta samo da kanta.
“Wannan abin ne ya fusata mutumin har ya sa hannu ya mare ta. Nan da nan kuwa mutanen da ke wurin suka nuna masa rashin dacewar abin da ya yi, inda wani a ciki ya fitar da hannu ya rama mata marin.
“Ba mu yi aune ba sai mutanen yankinsu suka zo suka far mana. Ka san mu ma ba za mu kyale su ba.”
Sai dai shi ma Dan Sanda ya yi karin haske game da yadda lamarin ya faru, inda ya bayyana cewa “Na sayi awarar Naira 300 sai na ba mai awarar Naira 500 sai ta ce ba canji.
“Sai na nemi ta ba ni kuɗin na nemo canjin sai ta hana ni. Wai a cewarta zan gudu da kudinta.
“To muna cikin wannan maganar ne sai wasu samarin yankin da ke can gefe suka taso suka sa baki suna cewa wai dama ni ba ni da mutunci da sauran munanan kalamai.
“Nan da nan wasu a cikinsu suka dauko katako suka fara dukana har suka fasa min kai.”
Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.
SP Kiyawa ya bayyana cewa yayin da rikicin ya barke ’yan sanda sun yi kokarin kwantar da tarzomar, sai dai samarin yankin sun riƙa jifansu da duwatsu, wanda a sanadiyyar hakan aka kama mutane kusan 30.
A cewar Kiyawa, rundunar na ci gaba da gudanar da bincike don hukunta wadanda ke da hannu a lamarin.
Kiyawa ya kara da cewa, a yanzu haka al’amura sun koma daidai a wadannan garuruwan, inda rundunar ta nemi al’umma da su rungumi al’adar zaman lafiya da juna don samun kwanciyar hankali da karuwar arziki.