Rikici da talauci ke haifar da tauye haƙƙin ɗan Adam a Yobe – NHRC
Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Ƙasa (NHRC), ta ce rikice-rikice da matsalolin tattalin arziƙi suna ƙara haddasa take haƙƙoƙin ɗan Adam a Jihar Yobe.
Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Ƙasa (NHRC), ta ce rikice-rikice da matsalolin tattalin arziƙi suna ƙara haddasa take haƙƙoƙin ɗan Adam a Jihar Yobe.
Kodinetan hukumar a jihar, Labaran Babangida ne, ya bayyana hakan yayin bikin Ranar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Duniya da aka yi a Damaturu.
- ’Yan sanda sun kama mutum 3 da jabun kuɗi N129bn a Kano
- Matashi ya daɓa wa mahaifiyarsa wuƙa a Bayelsa
Ya ce, “A yanzu haka, mun tattara ƙararraki kusan 265 na take haƙƙin dan Adam a jihar.”
Babangida ya ƙara da cewa matsalolin tattalin arziƙin duniya da rikice-rikicen tsaro suna jawo ƙara tauye haƙƙoƙin bil adama idan ba a ɗauki mataki ba.
Ya ce a jihohin Borno, Adamawa, da Yobe, rikicin Boko Haram na fuskantar yawan take haƙƙin ɗan Adam.
Babban jami’in wayar da kai na Hukumar Raya Ci gaban Al’umma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP), Kalu Okey, ya ce rikice-rikice suna taimakawa wajen tauye haƙƙoƙin jama’a.
A cewarsa, rikice-rikicen da ba a shawo kansu ba suna jawo karya dokokin ƙasa da kuma hana jama’a samun haƙƙinsu yadda ya kamata.
Don haka, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar an kare haƙƙoƙin jama’a.