Rikici na kara zafi tsakanin Kwankwaso da Ganduje a APC

Biyo bayan wutar rikicin shugabanci da ta dade tana ruruwa a jam’iyyar APC a Kano, a makon jiya ne kuma uwar jamiyyar ta kasa ta tabbatar da shugabancin riko a hannun Injiniya Yahaya Bashir Karaye, wanda ke goyon bayan bangaren Gandujiya a jihar, wannan mataki dai shi ya tabbatar da dakatar da na hannun daman […]

Rikici na kara zafi tsakanin Kwankwaso da Ganduje a APC

Biyo bayan wutar rikicin shugabanci da ta dade tana ruruwa a jam’iyyar APC a Kano, a makon jiya ne kuma uwar jamiyyar ta kasa ta tabbatar da shugabancin riko a hannun Injiniya Yahaya Bashir Karaye, wanda ke goyon bayan bangaren Gandujiya a jihar, wannan mataki dai shi ya tabbatar da dakatar da na hannun daman Sanata Kwankwaso, Umar Haruna Doguwa daga shugabancin jam’iyyar, lamarin da ke nuni da cewar an kakkabe hannun bangaren Kwankwasiyya daga shugabancin jamiyyar a Kano sannan kuma aka maye gurbinsa da mai goyon bayan Gandujiyya.

Wannan mataki dai ya kara iza wutar sabanin da ke tsakanin shugabannin biyu, sannan ya harzuka daruruwan ‘yan Kwankwasiyya har ta kai wasu na ficewa daga jam’iyyar tare da yin kakkausar suka ga shugabancin jam’iyyar wanda suke ganin bai yi musu adalci ba.

Haka zalika shi ma madugun darikar ta Kwankwasiyya, tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya aika da sako ga magoya bayansa, yana mai nuna takaici bisa wannan al’amari. Tun bayan daukar wananan mataki bangaren Kwankwasiyya a Jihar Kano ya gabatar da wani taron magoya baya har ma an jiyo na hannun daman Sanata Kwankwaso Kwamared Aminu Abdulsalam na cewa sun yi Allah wadai da wannan dauki-dora da aka yi musu.

 

Haka kuma lamarin ya ja hankalin masana siyarar kasar, inda wadansu ke ganin cewa sauke Doguwa ya ci karo da kundin tsarin mulkin ita kanta jam’iyyar APC, don haka wasu ke ganin cewa an yi kitso da kwarkwata a wannan matakin.

To amma sai dai kuma a ranar Talatar da ta gabata ne Gwamnatin Kano ta bakin Kwamishinan yada labarai na jihar, Kwamared Muhammed Garba, ta mayar da martani cikin wani taron manema labarai da suka gabatar, haka kuma tun da fari gwamnatin Kano ta lashi takobin daukar matakin ladaftarwa a kan Sanata Kwankwaso matukar bai nemi gafarar Shugaba Muhammadu Buhari ba, bisa zarginsa da ya yi da hannu cikin wannan lamari da suka ce murdiya ce aka yi musu.

Wannan al’amari ne ke ci gaba da dumama yanayin siyasar jihar ta Kano, sannan kuma hakan na zuwa ne kwanaki kadan da gabatar da gangamin tarbar Kwankwaso a Kano, lamarin da shi ma ake ganin zai kara iza wutar siyasar da ta riga ta zafafa.