Rikici na neman kunno kai a Saudiya

A cikin makon da ya gabata ne, ‘yan sandan Saudiya suka kama manyan jami’an gwamnatin kasar da ‘yan kasuwa, wadanda duk suna da alaka da gidan sarauta. Wannan kame-kamen dai ya biyo bayan umarnin Yarima mai jiran gadon kasar ne, Mohammed bin Salman, da mahaifinsa, sarki Salman. Wannan dambarwar dai, yariman, wanda ake wa lakabi […]

Rikici na neman kunno kai a Saudiya

A cikin makon da ya gabata ne, ‘yan sandan Saudiya suka kama manyan jami’an gwamnatin kasar da ‘yan kasuwa, wadanda duk suna da alaka da gidan sarauta.

Wannan kame-kamen dai ya biyo bayan umarnin Yarima mai jiran gadon kasar ne, Mohammed bin Salman, da mahaifinsa, sarki Salman.

Wannan dambarwar dai, yariman, wanda ake wa lakabi da MBS, ne ke jagorantarta da nufin yaki da cin hanci da rashawa, duk da cewa wasu na ganin cewa kawai yariman yana yin haka ne domin ya danne abokanan hamayyarsa, masu jiran gadon sarautar.

Daga cikin wadanda ake damke akwai hamshakin dan kasuwar nan Yaima Alwaleed bin Talal, wanda shi ne shugaban Kingdom Holding mai jarin kimanin Dala biliyan $10, da tsohon gwamnan Riyadh, Yarima Turk Bin Abdullah, wanda ake zargi da ba kamfaninsa kwangila, da yarima Turki Bin Nasser da Ministoci hudu, da wasu tsofaffin ministoci.

Yarima Alwaleed shi ne babba kuma fitaccen dan kasuwa a fadin kasar Saudiya baki daya, kuma yana da hannun jari a kamfanonin Citigroup da Twitter.

Hakanan kuma, am kama Bakr bin Laden, shugaban kamfanin gine-gine na Binladin, da shugaban gidan Talabijin din MBC, Alwaleed al-Ibrahim.

Shi dai wannan sabon shirin na yaki da cin hanci, wanda ake yarima mai jiran gadon ne ke shugabanta, wasu masu sharhi akan al’amura suna ganin, dan shekara 32 din zai yi amfani da hukumar ne kawai domin ya gyara hanyar zama sarki, ta hanyar danne duk wani yarima mai jiran gadon.

Wani Farfesa a jami’ar Georgetown, mai suna Colin Kahl ya shaida wa kafar yada labarai ta bod

Cewa “Za a iya kama duk wani jami’in gwamnati ko dan kasuwa a yaki da cin hanci. Kuma wannan al’amarin da ya faru ya fi kowane al’amari tayar da kura a cikin shakara 50 da suka wuce a tarihin Saudiya,” inji Colin

Shi ma Farfesa Abdeslam Maghraoui, masanin harkokin siyasa a jami’ar Duke, ya aike wa kafar bod cewa “Kama manyan jami’an gwamnatin makusanta gidan sarauta ba karamin abu ba ne, kuma irin wannan lamarin zai iya janyo matsala babba a kasar.

“Ganin cewa Bin Salman yarima ne mai jiran gado har yanzu, gadon mahaifinsa idan ya rasu ko ya yi murabus, ba zai zo cikin sauki ba saboda irin wannan lamarin,” inji shi.