Rikici ya ɓarke tsakanin ’yan kasuwar Potiskum a Yobe

Rikicin shugabanci ya kawo rabuwar kai a haɗaɗɗiyar ƙungiyar ’yan kasuwa da ke Potiskum a Jihar Yobe

Rikici ya ɓarke tsakanin ’yan kasuwar Potiskum a Yobe

Kokarin neman madafun iko ya haddasa rikici a Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa ta Garin Potiskum (UMAPO) da ke Jihar Yobe bayan zargin ƙarewar  wa’adin shugabanninta na yanzu.

Shugaban kwamitin amintattun kungiyar, Alhaji Yahya Baban Talaka, ya ce kundin tsarin mulkin kungiyar ya tanadi cewa a rusa shugabannin zartaswa watanni uku kafin zabe ba wai shugaban ya yi gaba kansa ba.

A cewarsa, “kundin tsarin mulkin ƙungiyar ya tanadi cewa duk mamban da ke son tsayawa takarar kowane mukami, to matuƙar yana riƙe da wani matsayi a ƙungiyar, ya zama wajibi ya yi murabus.

“Idan kuma ba zai tsaya takara ba, to zai ci gaba har zuwa ranar da za a rantsar da sabbin shugabannin zartaswa,” in ji Alhaji Yahya.

A cewarsa kamar yadda kundin tsarin mulkin kungiyar ya tanada, shugaban ƙungiyar ba shi da hurumin rusa kwamitin amintattunta.

Don haka yanzu haka lamarin na gaban majalisar Ƙaramar Hukumar Potiskum wanda su ke da wuƙa da nama dangane da dukkan lamarin ƙaramar hukumar.

Rikicin ya kunno kai ne bayan da shugaban ƙungiyar mai barin gado, Alhaji Nasiru Mato, ya sanar cewa ya rusa mambobin kwamitin amintattu, wanda ya haifar da ruɗani tsakanin shuwagabanni da amintattun mungiyar.

Da Aminiya ke tuntubar shugaban ƙungiyar, Alhaji Nasiru Mato, a kan wannan lamari, sai ya amsa da cewar, “ai zance kawai masu ƙoƙarin haddasa rikici a wannan ƙungiya suke yi, domin kuwa wa’adinsu ba zai cika ba har sai ranar 7 ga watan Nuwambar wannan shekara ta 2024.

“Haka nan tsarin mulkinmu na Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa ta Potiskum (UMAPO) ya nuna ƙarara cewar, babu batun tsarin nada riƙon ƙwarya, daga zaɓe ne sai rantsarwa kawai.”

A cewarsa, “masu wancan furuci suna yi ne domin tayar da fitina da nufin ci ma buƙatarsu ba ta naɗa shugabannin riƙo kafin a gudanar da zaɓe, alhali kundin tsarin mulkin ƙungiyarmu bai tanadar da wannan tsari ba.

“Shugabannin da ke suna kai ne za a yi zaɓe kwana ɗaya ya rage ga cikar wa’adinsu wato daga zabe sai rantsarwa.”

Ya kara da cewa “waɗanda ke ƙoƙarin kawo rikici a ƙungiyar suna ganin wataƙila idan aka yi zaɓe ba za su kai labari ba, alhali malam bahaushe kan ce ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi.”

Alhaji Nasiru Mato ya ci gaba da cewar, “a yanzu haka maganar tana gaban majalisar karamar hukumar Potiskum kuma jami’an tsaron da ke cikin garin na Potiskum su ma suna lura da wannan lamari.”

Ya ce, don haka a halin da ake ciki suna jiran sakamakon hukuncin da majalisar ƙaramar hukumar don sanin makomar wannan dambarwa.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja