Rikici ya barke a APC reshen Sakkwato
Wani jigo a rusashiyar CPC a Jihar Sakkwato, kuma tsohon dan takarar Gwamnan a APC a jihar, Farfesa Muhammad Lawal Bashir ya zargi gwamnatin jihar a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da rashin yi wa ’ya’yan tsohuwar Jam’iyyar CPC adalci tare da kin cika musu alkawuran da aka yi a rubuce kafin kafa gwamnatin. […]

Wani jigo a rusashiyar CPC a Jihar Sakkwato, kuma tsohon dan takarar Gwamnan a APC a jihar, Farfesa Muhammad Lawal Bashir ya zargi gwamnatin jihar a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da rashin yi wa ’ya’yan tsohuwar Jam’iyyar CPC adalci tare da kin cika musu alkawuran da aka yi a rubuce kafin kafa gwamnatin.
“Gwamnan bai yi mana adalci ba, na kai korafi wajen shugaban jam’iyya ta kasa ya ce in dawo mu zauna da Gwamna, na rubuta wa Gwamna takarda amma har yanzu da nake magana ba wanda ya ce min ci kanka, dole ne mu fadi don kowa ya sani” inji shi
Farfesa Bashir ya ce cikin mukamai 69 da aka zaba don wakiltar jama’a da suka hada da Gwamna da Mataimakinsa da ’yan majalisar jiha da na tarayya da shugabannin kananan hukumomi babu wani dan asalin tsohuwar Jam’iyyar CPC a cikinsu.
Ya cewa cikin mukamai 88 da Gwamna Aminu Tambuwal ya nada, guda ne kacal ya bai wa dan CPC, wanda ko shi asalinsa dan PDP ne ya canja sheka zuwa CPC, wato Alhaji Ibrahim Magaji Gusau, Mai Bai wa Gwamna Tambuwal shawara kan harkokin siyasa.
“Da wannan muka yi farin ciki da kwamitin da Shugaba Buhari ya sanya don sasanta ’ya’yan jam’iyya kuma za mu mika masa korafinmu bayan mun sanar da jama’a rashin adalcin da aka yi mana bayan tsoratarwa da musgunawar da muke sha tsawon lokaci kamar ba da mu aka kafa gwamnatin ba,” Farfesa ya shaida wa taron manema labarai da ya kira a Sakkwato.
Da yake mayar da martani a hedikwatar Jam’iyyar APC ta Jihar Sakkwato, Mai Bai wa Gwamnan shawara kan lamurran siyasa, Alhaji Ibrahim Magaji Gusau ya musanta zarge-zargen da Farfesa Bashir ya yi ga gwamnati mai ci a jihar, inda ya ce wadannan zarge-zarge ba su da tushe yanayi ne don ya ga kamar an manta da shi tun da siyasa ta karaso mutane su san da shi.
Ya zargi Farfesa Bashir da kawo rudani a APC ganin cewa ya hada kai da wadansu jama’a suna kalubalantar gwamnatin Tambuwal a kotuna daban-daban kuma ba su yi nasara ba.