Rikici ya barke a garin Kidal na kasar Mali
Fada da manyan bindigogi ya barke a garin Kidal na Arewacin kasar Mali. ’Yan tawayen kasar Mali na da karfi a garin Kidal, sai dai sojoji Mali suna sa ran sake kwato shi, inji gidan rediyon BBC Landan.A ranar Litinin da ta gabata ne ’yan tawayen suka sako sojoji 28 da suka yi garkuwa da […]
Fada da manyan bindigogi ya barke a garin Kidal na Arewacin kasar Mali. ’Yan tawayen kasar Mali na da karfi a garin Kidal, sai dai sojoji Mali suna sa ran sake kwato shi, inji gidan rediyon BBC Landan.
A ranar Litinin da ta gabata ne ’yan tawayen suka sako sojoji 28 da suka yi garkuwa da su lokacin ziyarar da Firayi-Ministan kasar Moussa Mara a ranar Asabar.
’Yan tawayen sun sace sojojin ne bayan sun je sun gana da Firayi-Ministan wanda ke ziyararsa ta farko a Arewacin kasar tun hayewarsa kujera a watan jiya.
Wakilin BBC ya ce babu tabbas a kan ko an tsare su ne a ofishin Gwamna – wanda har yanzu ke hannun ’yan tawayen – ko kuma an dauke su zuwa wani wuri na daban.
Ma’aikatar Tsaron kasar Mali ta ce sojoji takwas ne aka kashe, aka kuma kashe Abzinawa 28 a gwabzawar da suka yi a garin Kidal, wanda wani bangarensa ke hannun ’yan tawayen.
An sanya dokar hana fita a Kidal yayin da kuma jirage masu saukar ungulu ke ta shawagi a sararin samaniyar garin.
Wani boren da Abzinawa suka yi a Arewacin Mali a shekarar 2012 ne ya haifar da juyin mulki a kasar. Kuma a bara ne aka sake maido da mulkin farar hula bayan Faransa ta sa hannu domin kwantar da tarzomar, sai dai duk da haka masu kishin Musulunci da ’yan aware suna da karfi a wasu wurare na sassan yankin.