Rikici ya barke a Jam’iyyar APC reshen Filato

Rikici ya barke a Jam’iyyar APC reshen Jihar Filato bayan da tsohon shugaban riko na jam’iyyar Sanata John Shagaya ya jagoranci wani taron shugabannin jam’iyyar inda suka ba da sanarwar sauke shugaban jam’iyyar na jihar Mista Letep Dabang tare da nada Mista Amos Gombi sabon shugaba.Sanata John Shagaya ya jagoranci taron ne a ofishin jam’iyyar […]

Rikici ya barke a Jam’iyyar APC reshen Filato
Rikici ya barke a Jam’iyyar APC reshen Filato

Rikici ya barke a Jam’iyyar APC reshen Jihar Filato bayan da tsohon shugaban riko na jam’iyyar Sanata John Shagaya ya jagoranci wani taron shugabannin jam’iyyar inda suka ba da sanarwar sauke shugaban jam’iyyar na jihar Mista Letep Dabang tare da nada Mista Amos Gombi sabon shugaba.
Sanata John Shagaya ya jagoranci taron ne a ofishin jam’iyyar da ke Kalwa House a garin Jos a ranar Litinin, inda ya karanta wasikar da suka samu daga kwamitin sauraron koke-koken zaben shugaban jam’iyyar da aka gudanar a jihar daga sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke dauke da sanya hannun tsohon sakataren riko na jam’iyyar ta kasa Alhaji Tijani Musa Tumsah.
Sanata Shagaya ya ce a wasikar an ce zaben da aka yi wa Letep Dabang ba a yi shi a kan ka’ida ba.
Ya ce a koken an ce kafin a zabi Dabang yana yi wa wani Sanata aiki wanda ba dan Jam’iyyar
APC ba ne, inda bayanai suka nuna Dabang ya karbi albashin watan Maris na bana kan wannan aiki da yake yi.
Ya ce don haka kwamitin ya soke zaben Dabang tare da maye gurbinsa da Mista Amos Gombi a matsayin shugaban jam’iyyar.
To, amma a nasu bangaren a taron da suka gudanar a ofishin jam’iyyar da ke Dogon karfe a ranar Talata, shugabannin Jam’iyyar APC na jihar da na kananan hukumominta sun bayyana goyon bayansu ga shugabancin Letep Dabang.
Mataimakin shugaban Jam’iyyar APC na jihar Fanmak Enoch ya ce taron da Sanata Shagaya ya jagoranta wasan kwaikwayo ne.
Ya ce tsohon shugaban riko na kasa na jam’iyyar Cif Bisi Akande ya riga ya rantsar da Letep Dabang da sauran shugabannin jam’iyyar na jihohi, kuma tun lokacin uwar jam’iyyar ta kasa ke aiki tare da shi, “amma abin dariya sai ga wasu mutane na kokarin nada sabon shugaba a nan Jos,” inji shi.