Rikici ya barke tsakanin DSS da EFCC

Da sanyin safiya ne jami’an DSS suka je ofishin na EFCC suka hana jami’an da ake aiki a wurin shiga cikin harabar.

Rikici ya barke tsakanin DSS da EFCC

Jami’in hukumar DSS

An samu rikici tsakanin Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS da jami’an EFCC bayan da jami’an DSS suka hana ’yan EFCC shiga ofishinsu.

Rikicin ya samo asali ne a safiyar Talata, kan mallakar ginin ofishin da hukumomin biyu suke, a kan Titin Awolowo da ke Jihar Legas.

Aminiya ta gano cewa da sanyin safiya ne jami’an DSS suka hana ’yan EFCC da ake aiki a wurin shiga cikin harabar.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce ko da jami’an hukumarsa suka zo aiki da safe, DSS sun hana su shiga harabar.

Wakilanmu ya nemi samun karin bayani daga kakakin DSS, Peter Afunanya, amma bai tabbatar ko kore faruwar hakan ba.

Sai dai ya jaddada cewa hukumarsa ce ke mai mallakar ofishin, kuma hukumomin biyu sun shafe kusan shekaru 20 suna zama tare a harabar.

Ya ce hukumarsa ce asalin mai wurin, don haka ba daidai ba ne a  ofishin EFCC ne, jami’an DSS suka tare ba.

Kotu ta bayar da umarnin bai wa Hamdiyya tsaro

Yadda na taso daga almajiranci na zama shugaban NNPCL – Kyari

Shugaban ’yan sandan Mopol na Legas ya Musulunta a Kano

Mun daidaita tsakaninmu ni da Alpha – G-Fresh