Rikici ya barke tsakanin magoya bayan NNPP da APC a rumfar zabe a Kano
Tarzoma ta balle tsakanin magoya bayan jam’iyyu
Ana shiga halin dar-dar a yankin Chiranci cikin Karamar Hukumar Gwale, Jihar Kano, bayan rikici da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da NNPP.
Chiranci na daga cikin yankunan da aka fi barazanar rikici a jihar, kuma nan ce rumfar shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas da kuma dan takarar Gwamna na NNPP, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida).
Rikicin ya fara ne bayan hudu daga akwatunan zaben yankin sun kammala hada sakamakonsu, har ma wasu wakilan jami’iyyu sun rattaba hannu a kan takardar sakamakon.
Duk da dai babu cikakken bayani game da dalilin aukuwar rikicin, amma jami’an tsaron da ke wurin sun yi kokarin kashe wutar rikicin.
Ko a 2019 an samu tarzoma tsakanin magoya bayan jami’iyyu a yankin.
Amma 2023 INEC ta raba akwatin inda ta maida Abba Gida-Gida da iyalansa zuwa sabon akwatin da ta kirkiro wanda bai da nisa da tsohon akwatin.