Rikici ya kaure a Majalisar Wakilai

Yan Majalisar Wakilai ta Tarayya sun so ba hammata iska a lokacin da aka ambaci shugaban marasa rinjaye a majalisar Femi Gbajabiamila a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye, yayin aka ambaci Leo Ogor da ‘mataimakin shugaban marasa rinjaye.’ Ana muhawara kan harin da ’yan sanda suka kai ga Sanata Magnus Abe daga Jihar Ribas ne […]

Rikici ya kaure a Majalisar Wakilai
Rikici ya kaure a Majalisar Wakilai

Yan Majalisar Wakilai ta Tarayya sun so ba hammata iska a lokacin da aka ambaci shugaban marasa rinjaye a majalisar Femi Gbajabiamila a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye, yayin aka ambaci Leo Ogor da ‘mataimakin shugaban marasa rinjaye.’ Ana muhawara kan harin da ’yan sanda suka kai ga Sanata Magnus Abe daga Jihar Ribas ne sai Gbajabiamila ya bayyana Ogor da mataimakin shugaban marasa rinjaye. Wannan ya harzuka shugaban masu rinjaye Mulikat Akande da Ogor suka mika tsaye suna ba su yarda ba, inda magoya bayan Jam’iyyar PDP suka goya musu baya. Ganin haka ne sai magoya bayan APC suka mayar da martani, kuma suka nufi inda Gbajabiamila yake don ba shi kariya, inda aka shafe kusan minti 20 ana hatsaniya.
Tambuwal ya dauki lokaci kafin ya shawo kan wakilan majalisar, inda ya rarrashi magoya bayan APC suka dakatar da yunkurinsu na sauya shugabannin majalisar don girmama umarnin kotu. Ya ce a matsayinsu na masu kafa dokoki bai kamata su karya doka ba.