Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa

Rikicin ya yi sanadin mutuwar wai mace mai juna biyu a yankin.

Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa

‘Yan sanda

Wani rikicin ƙabilanci da ake zargin ya auku tsakanin Fulani makiyaya da wasu Gwarawa ya yi ajalin wata mai juna biyu, Azumi Allah Gaba da wasu mutum 10 a garin Farin Duse da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa ta Jihar Nasawara.

Binciken Aminiya ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da wani makiyayi ya tsinko ganyayyaki a reshen wata bishiyar mangwaro yayin da ya fita kiwon shanunsa

Sai dai wani mazaunin yankin da ya hango makiyayin ya yi ƙoƙarin hana shi, lamarin da ya haifar da cacar baki a tsakaninsu.

Bayanai sun ce cacar bakin ce ta ƙazanta har makiyayin ya harbe mutumin nan take, lamarin da ya haddasa mummunan rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoman Gwari a yankin.

Wani ganau da ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa: “Rikicin ya fara ne da misalin ƙarfe 6 na safe a ranar Lahadi, 9 ga watan Maris, 2025, har zuwa yammacin Talata.

“Jami’an tsaro sun tabbatar da zaman lafiya, amma har yanzu garin Gwari babu kowa, kuma ana jin ƙarar harbe-harbe a Farin Ruwa Duse.

“An ƙone gidaje sama da 20 tare da lalata wani ofishin ’yan sanda da ke yankin.”

Wasu bayanai sun nuna cewar an lakaɗa wa DPO duka, sannan aka lalata babur ɗinsa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, ta tabbatar da mutuwar Azumi Allah Gaba da jaririnta da ke cikinta, tare da wasu mutane.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Nansel Rahman, ya fitar, ya bayyana cewa an kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a rikicin.

Ya tabbatarwa da jama’a cewa jami’an tsaro sun shawo kan lamarin, kuma ana ci gaba da bincike don kama duk waɗanda ke da hannu a lamarin.