Rikicin Afirka ta Tsakiya ya salwantar da rayukan ’yan Najeriya 83
A kalla ’yan Najeriya mutum 83 suka rasa rayuknsu a Bangui babban birnin kasar Afirka ta Tsakiya, inda aka shafe watanni ana fafata fada da rikicin siyasa, kamar yadda wani shugaban al’umma ya bayyana wa Aminiya. Wannan kasa ta dade cikin rikici, tun bayan samun ’yancin kanta a shekarun 1960, amma rikicin baya-bayan nan ya […]

A kalla ’yan Najeriya mutum 83 suka rasa rayuknsu a Bangui babban birnin kasar Afirka ta Tsakiya, inda aka shafe watanni ana fafata fada da rikicin siyasa, kamar yadda wani shugaban al’umma ya bayyana wa Aminiya. Wannan kasa ta dade cikin rikici, tun bayan samun ’yancin kanta a shekarun 1960, amma rikicin baya-bayan nan ya auku ne a sanadiyyar juyin mulkin da Shugaban ’yan Tawaye Michel Djotodia ya yi wa Francois Bozize a watan Maris din bana.
Wannan rikici ya zama na kabilanci da addini, tunda Djotodia ya kasance Musulmin farko da shugabanci kasar da mafi yawan al’ummarta Kiristoci ne.
Shugaban ’yan Najeriya da ke zaune a kasar, Muhammad Kalanbai, wanda ya gana da Aminiya ta wayar tarho, ya bayyana cewa mafi yawan ’yan Najeriyar da aka kashe sun fito ne daga Arewacin Najeriya
“a daidai lokacin da nake magana da ku, akwai gawarwakin ’yan Najeriya Musulmi 16 a masallacin Ali Baglo da ke Bangui, wadanda ba a binne su ba, saboda rikici,” inji Kalanbai, wanda shi ne shugaban ’yan Arewacin Najeriya da ke zaune a kasar.
Ya kuma bayyana cewa magoya bayan Bozize, hambararren shugaban kasar, sun kashe a kalla mutum 67 a makon da ya gabata. “A daidai lokacin da muke tattaunawa da ku za ku iya jin karar harbe-harben bindiga. Ni ma da kyar na sha da an kashe ni tun jiya,” inji shi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuter, ya ruwaito yadda tashe-tashen hankula suka haifar da asarar rayuka, kuma manema labarai sun ga yadda aka cinna wa masalla wuta, aka wawushe gidajen al’umma, tare da kona motoci.
Kalanbai ya ce, sojojin Faransa ba sa bai wa fararen hula kariya, sai mabiya Bozize, wadanda ke kashe Musulmi, inda suke sarar mutane da adduna da sauran miyagun makamai. Don haka a cewarsa, ‘Musulmi ’yan Najeriya na ta guduwa zuwa ofishin jakadancin kasarsu da ke Bangui don neman kariya.
Ya kuma yi roko ga gwamnatin Tarayya da ta kwashe mutzanenta zuwa gida.
Ministan Tsaro na Faransa ya ce tilas sojojin da ke biyayya ga Shugaban wucin gadi na kasar Afirka ta Tsakiya, Michel Djotodia su koma bariki, sannan mayakan da ke fafatawa da su, su mika makamansu. Kuma Gwamnatin Farasansa ta bukaci kungiyar Tarayyar Afirka da ta kara yawan sojojin kawo zaman lafiya, daga dubu biyu da 500 zuwa dubu shida.
Shi kuwa babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya, Ban Ki-moon cewa ya yi, akwai bukatar sojojin kiyaye zaman lafiya har dubu tara, da za su shawo kan rikicin Afirka ta Tsakiya, kuma yana fatan aikin ya koma karkashin kulawar majalisarsa kaco-kam.
An kashe sojojhin Faransa biyu a wani karon batta da aka yi a birnin Bangui da ke Afirka ta tsakiya, kamar yadda aka bayar da sanarwa daga ofishin Shugaban kasar Faransa Francois Hollande, inda ya ga wallen kalubalen da kasarsa za ta fuskan a daukin sojan da ta a wannan kasar da babu doka.
Shugaba Hollande ya kai ziyara kasar Afirka ta Tsakiya bayan an kammala bikin bankwana da gwarzon Afirka ta Kudu, Marigayi Nelson Mandela.