Rikicin Ansaru da ’yan bindiga ya sa mutanen Birnin Gwari hijira
Mazauna garin Tsohuwar Kuyello a yankin Birnin Gwari na barin gidajensu a sakamakon rikicin ’yan ƙungiyar Ansaru da barayin daji a yankin.
Mazauna garin Tsohuwar Kuyello a yankin Birnin Gwari na barin gidajensu a sakamakon rikicin ’yan ƙungiyar Ansaru da barayin daji a yankin.
Bayanai daga yankin na nuna cewa barayin dajin sun shiga cikin garin ne a ranar Lahadi da misalin karfe 3 na rana suna bin gidaje suna fashi.
Makonni biyu kafin nan sun yi fada da ’yan ƙungiyar Ansaru a cikin daji wanda hakan ya sa ’yan Ansarun janyewa daga garin.
Majiyarmu dak e a yankin ta tabbatarwa Aminiya cewa ’yan fashin daji sun yi wa ’yan Ansaru kwanton ɓauna ne har suka halaka biyar daga cikinsu.
- Zaben Kano: Ranar Alhamis Kotun Ƙoli za ta saurari shari’ar
- An tsare matashi kan tsokanar budurwa da ‘kin iya Kunu’ a Kano
Hakan ne ya sa ’yan Ansaru barin cikin garin a ’yan kwanakin nan wanda ya bai wa barayin damar shiga cikin garin suna cin karensu babu babbaka ta hanyar kwashe kayan abincin jama’a.
Babu labarin kisa ko sace mutane sai dai kurum ’yan fashin na ta barin wutar domin razana mazauna garin.
Wani mazaunin yankin Hadi Kuyello ya tabbatar ce da yawan barayin dajin sun rasa rayukansu a lokacin artabun da suka yi da ’yan Ansarun.
“A yanzu haka da nake magana da kai ’yan fashin dajin na cikin garin tsohuwar Kuyello, wanda hakan ya sa mazauna garin ke barin cikin garin domin tsirar da rayukansu.
“Saboda barayin na bi gida-gida ne suna sata tare da kwashe kayan abinci,” in ji shi.
Ya ce ana kwashe mata da yara da ke barin garin ne akan barbura a yayin da kuma wasu mazajen ke bi ta cikin dazuka domin tsirar da iyalansu.
Shugaban kungiyar kare muradun Birnin Gwari Ishaq Kasai ya tabbatar da lamarin inda ya ce mazauna yankin na ficewa ne domin tsirar da rayukansu.
Har yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar ko rundunar ’yan sandan jihar dangane da lamarin.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan ya ci tura kuma har ya zuwa lokacin aiko da da rahoton bai amsa sakon tes da aka aika masa ba.