Rikicin APC: Majalisar Kano ta bukaci uwar jam’iyya ta hukunta Doguwa

Majalisar ta bukaci uwar Jam’iyyar APC ta dauki matakin da ya dace kan Doguwa, saboda munanan dabi’unsa da kuma yadda wuce gona da iri.

Rikicin APC: Majalisar Kano ta bukaci uwar jam’iyya ta hukunta Doguwa

Alhassan Doguwa

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta la’anci abin da ta kira aikin assha da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya aikata.

Majalisar ta bukaci hedikwatar Jam’iyyar APC ta kasa da kuma reshen Jihar Kano su dauki matakin da ya dace kan Doguwa, saboda munanan dabi’unsa da kuma yadda wuce gona da iri.

Majalisar ta sanarwar da Shugaban Masu Rinjaye, Labaran Madari, ya fitar, ta ce abin da Doguwa ya yi wa mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar, Murtala Garo, ya yi hannun riga da tsarin jam’iyyar.

A ranar Litinin ne dai rahotanni suka bulla cewa Doguwa ya kai wa Murtala Garo farmaki a lokacin taron jam’iyyar a gidan mataimakin gwamnan jihar, Nasir Gawuna.

Washegari, aka ruwaito dan Majalisar ya ci zarafin kakakin APC na Jihar, Ahmad Aruwa, gami da barazanar daukar mataki kan a tsohon sakataren gwamnatin jihar, Rabiu Bichi.

Dan majalisar ya kuma kai wa wani dan jarida hari yayin da yake ganawa da manema labarai a gidansa a ranar Talata.

A halin yanzu dai kotun Majisatare da ke Gyadi-gyadi a Kano ta umarci ’yan sanda su binciki zargin duk dan jairdar da ake zargin Doguwa ya yi.