Rikicin APC: Mun yanke kauna da gwamnatin El-Rufai – APC Akida

Ayayin da rikicin siyasa ke ci gaba da yin kamari a jam’iyar APC a Jahar Kaduna, yan APC Akida sun bayyana cewa daga yanzu sun yanke kauna da gwamnar Jahar, Nasir Ahmad El-Rufai. A cewarsu, sun dau matakin ne saboda nuna rashin amincewarsu da salon mulkinsa. Shugaban ‘Yan Akida na jahar, Tom Maiyashi ne ya […]

Rikicin APC: Mun yanke kauna da gwamnatin El-Rufai – APC Akida

Ayayin da rikicin siyasa ke ci gaba da yin kamari a jam’iyar APC a Jahar Kaduna, yan APC Akida sun bayyana cewa daga yanzu sun yanke kauna da gwamnar Jahar, Nasir Ahmad El-Rufai. A cewarsu, sun dau matakin ne saboda nuna rashin amincewarsu da salon mulkinsa. Shugaban ‘Yan Akida na jahar, Tom Maiyashi ne ya sanar da hakan a zantawarsa da manema labarai domin nuna rashin jin dadin su ga wasu matakai da gwamnatin ke dauka. Ya ce gwamnatin El-Rufai ba ta da wata manufa da ta wuce matsawa mutanen jahar da suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka zabi APC a shekarar 2015. “Yana musgunawa mutane tare da rusa rayuwar mutane da suka zabi APC. A yanzu gwamnatinsa ba ta da wata manufa sai matsawa mutane. Dubi yadda kwanan nan ya sauke hakimai da dakatai wanda hakan zai iya kawo rudani.

“Kowa ya san irin taimako da hakimai da dakatai ke badawa cikin al’ umma domin a samu zaman lafiya. Amma aka sauke su wai kawai saboda kudi. Nawa albashinsu yake dakaci bai wuci karbar naira 18,000 a wata ba, shi kuma Hakimi bai wuce naira dubu 50 ba.
“Akwai bayanai dake nuna cewa bayan hakimai zai waiwayi wasu sarakunan, wannan yasa muke masa kashedi da kada ma ya fara domin a shirye muke mu yake shi. Daga yanzu mun yanke kauna da shi da gwamnatinsa ba kuma za mu sake wata huldar siyasa da shi ba.
“Idan kuwa ya fito da doka da muka lura zata cutar da jama’armu ba za mu amince da ita ba. Domin ba zamu yarda ya sake cutar da mutanen mu ba,” inji shi.
Wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan jam’iyar APC Akida da suka rufawa Shugaban baya sun hada da Dan takarar gwamnar jahar a zaben 2015, Isa Ashiru Kudan da Sanata mai wakiltar yankin Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani da sauransu.
Amma fa Gwamnatin jahar ta bakin Kakakinta, Samuel Aruwan ta karyata zargin da ‘yan Akidar suke yi cewa gwamnatin na ta ci zarafin masarautun dake a jahar.
“Wannan zancen ba gaskiya ba ne domin gwamnati ba ta dauki matakin sauke hakimai da dakatai ba sai da ta tattaunawa da majalisar sarakunan jahar. Sannan manufarmu ita ce maido da martabar masarautunmu ba maida su baya ba,” inji shi Ya ce tuni sarakunan sun mako sabbin sunayen masu neman kujerun Hakimai da dakatai. “Wannan alama ce dake nuna Jama’a na tare da wannan gwamnati sannan kuma su ‘yan Akida dake wadannan maganganu suna yi ne kawai saboda siyasa, domin cimma wata manufa tasu,” inji shi