Rikicin APC ya dauki sabon salo a Jihar Sakkwato

Rikicin da ya dabaibaye Jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato ya dauki sabon salo bayan da bangaren da tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya kaddamar da shugabannin riko a ranar Lahadin da ta gabata. Wannan rikita-rikitar siyasa ta somo ne tun lokacin da Gwamna Wamakko ya canja sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC a […]

Rikicin APC ya dauki sabon salo a Jihar Sakkwato

Daruruwan magoya bayan Jam’iyyar APC a wurin kaddamar da shugabannin jam’iyyar banagren Bafarawa a Sakkwato a ranar Lahadin da ta gabata.Rikicin da ya dabaibaye Jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato ya dauki sabon salo bayan da bangaren da tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya kaddamar da shugabannin riko a ranar Lahadin da ta gabata.
Wannan rikita-rikitar siyasa ta somo ne tun lokacin da Gwamna Wamakko ya canja sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC a watan Oktoban da ya gabata.
Wata sanarwa dauke da sanya hannun Sakataren bangaren Bafarawa, Alhaji Lawali Tukur Faru, ta ce an nada shugabannin ne bayan tattaunawa a tsakanin jam’iyyun da suka narke a hadakar wato ANPP da CPC da ACN, inda jagoran APC a jihar na bangaren, Alhaji Attahiru Bafarawa ya amince da nada kwamitin rikon. Shugabannin sun hada da Abubakar Saddik Sanyinna (ANPP), shugaba da Alhaji Lawali Tukur Faru (CPC), Sakatare da Nasiru Kalambaina (ACN), Ma’aji da Alhaji Yusuf Dingyadi (ANPP), Sakataren Labarai da Nasiru Asara (CPC), Sakataren Tsare-Tsare.
Jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Gwamna Wamakko ta riga ta bayyana Alhaji Inuwa Abdulkadir da ’yan kwamitinsa tara a matsayin shugabannin riko a makon jiya, inda Alhaji Inuwa Abdulkadir, ya shaida wa manema labarai cewa “An nada mu ne mu jagoranci wannan sabuwar jami’yya domin aza ta a kan tubali mai inganci da zai sanya ta samu jagorori na kwarai.”
Ya ce a yanzu jam’iyyarsu ba ta da wani bangare sai dai masu son kawo cikas ga tafiyarta da suka karbo kwangilar rusa ta daga hannun gwamnatin PDP wadanda nan gaba kadan za su fallasa su don fadakar da jama’a.
Shugaban jam’iyyar na bangaren Bafarawa Alhaji Sadik Sanyinna ya shaida wa Aminiya cewa “Bisa umarnin uwar jam’iyyarmu ta kasa na kowace jiha ta kafa kwamitin rikon kwarya ne aka zabe ni a matsayin sabon shugaban APC a jihar nan, muna da takarda a rubuce daga uwar jam’iyya duk mai so za mu nuna masa.”
Ya kara da cewa ba wata jayayya da suke yi, su ne ’yan asalin Jam’iyyar APC, ba za a saba doka don wani ya shigo jam’iyyar balle ya tarwatsa shirinsu ba, “Sun zo suna fadin su ne masu jam’iyya bayan kafin su zo an kammala rubuta tsarin mulkinta, gwamna 11 kundin tsarin jam’iyya ya san da su, su ne jagoran tafiya, mu ba jahilai ba ne balle a  yi mana hawan kawara,” inji shi. Ya ce shekara bakwai suka yi suna jayayya da wannan (Gwamna Wamakko) kuma yanzu ya zo bai nemi lalamar su ba, ya kamata ya san jam’iyyarsu ba irin PDP ce ba da ake karyawa ko ba gaba.