Rikicin ASUU da gwamnati

Ba don yajin aikin ba da jami’o’in Najeriya sun durkushe.

Rikicin ASUU da gwamnati

A ranar Litinin da ta gabata ce Kwamitin Zartarwa na Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ya sanar da ci gaba da yajin aikin malaman jami’o’i na mako takwas.

Wannan zarcewa da yaji aiki na zuwa ne bayan jami’o’in Najeriya sun kwashe wata daya a kulle a wani yajin aiki da malaman suka ce da ma na gargadi ne da aka fara a watan Fabrairu.

Bukatun da malaman suke so gwamnati ta cika musu sun hada da fitar da kudaden raya jami’o’in gwamnati da wasu kudaden alawus-alawus na mambobinsu da amincewa da tsarin biyansu albashi na UTAS maimakon na IPPIS da kuma aiwatar da bukatun yarjejeniyarsu da gwamnati ta shekarar 2009.

A makon jiya ne Darakta-Janar na Hukumar Kula da Fasahar Zamani (NITDA), Inuwa Kashifu Abdullahi ya ce tsarin na UTAS da Kungiyar ASUU ke muradi a yi amfani da shi, ya fadi gwajin nagarta da hukumarsa ta yi, lamarin da ASUU ta mayar da martanin cewa ba haka ba ne.

Batun yajin aikin Kungiyar ASUU dadadden abu ne tun bayan komawar kasar nan kan turbar mulkin dimokuradiyya, inda tun a shekarar 1999 ta fara tafiya yajin aiki amma har yau ba a samu daidaito ba, duk da cewa malaman suna cewa an dan samu ci gaba.

Ana mayar da karatunmu baya Dalibai

Aminiya ta tattauna da wasu iyaye da dalibai, wadanda yawancinsu suka nuna rashin jin dadinsu game da lamarin, inda suka yi kira ga gwamnati da ta yi duba a kan lamarin malaman jami’oi domin su koma bakin aikinsu.

Maryam Ahmad Nasidi, daliba a Jami’ar Bayero, ta ce ta shiga halin damuwa da jin wanann labari.

“Ba zan iya bayyana damuwar da nake ciki ba, domin idan kika kalli wannan yajin aikin mu dalibai ne muke cutuwa domin mu muke komawa baya. Ana kara tsawaita mana lokacin karatunmu.

“Idan dalibi zai kammala karatunsa a shekara hudu to sai ki ga sai ya shafe shekara biyar ko shida kafin ya kammala.”

Wani dalibi mai suna Ali Aminu ya bayyana takaicinsa game da yadda yajin aikin ya hana su rubuta jarrabawarsu a kan lokaci.

“Abin takaicin shi ne muna gab da za mu fara rubuta jarrabawarmu malaman nan suka tafi yajin aikin.

“Yanzu sun bar mu da kaya a kanmu. Da a ce mun gama rubuta jarrabarwarmu to da damuwarmu za ta zo da sauki.”

Shi kuwa Ahmad Zubair ya zargi gwamnati da malaman jami’oi ne saboda kasa samun matsaya da suka yi da rashin.

“Ni abin da yake ba ni haushi game da wanann yajin aiki da malamai ke yi shi ne ba su tausayawa daliban kasar nan.

“Idan kin duba dukkanin bangarorin biyu na malaman da gwamantin ba su duba maslahar mu daliban kasar nan.

“Idan kika duba kowane bangare bukatunsa ne kawai a gabansa. Amma dalibai ko oho.

“Kuma wannan ya samu ne saboda babu ’ya’yansu a cikin daliban domin daga gwamnatin har malaman jami’o’in ’ya’yansu a kasashen waje suke karatu don haka babu ruwansu da tausaya wa daliban kasar nan.”

Shi ma wani dalibai mai suna Ismai Ibrahim da ke karatu a Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Gusau cewa ya yi yana mamaki yadda matsalolin Najeriya ba sa karewa.

“Mun fara karatu ke nan aka tafi yajin aiki. An ce wata daya, kwatsam wai an kara mako takwas. Ya kamata dai a samu maslaha.”

Ba ma jin dadin yajin aikin —Iyaye

Aminiya ta zanta da wasu iyaye, inda suka nuna rashin jin dadinsu. Malam Umar Amin, wani mahaifi da ke da ’ya’ya biyu a jami’a, ya ce “a gaskiya yajin aiki ya dame mu domin kullum so muke mu ga ’ya’yanmu sun kammala karatu sun kama aiki, amma a yanzu ga su nan an bar mana su a gabanmu ba karatu ba aikin yi.

“Sai dai yara su yi ta gararamba a gari, wanda hakan zai iya kai su ga fadawa wasu halaye marasa kyau.”

“Ita ma wata mahaifiya da take da da daya a jami’a, sannan take da guda daya da take jiran samun gurbin karatu, ta ce da ma ta dade tana jin labarin yadda yajin aikin ke jefa karatun yara cikin damuwa, kuma ita ma yanzu ta gani.

A cewarta, bai kamata a ce a yi ta magana daya ba na tsawon lokacin nan amma babu matsaya.

Ba laifinmu ba ne —Malaman jami’a

Sai dai a daidai wannan lokacin da iyayen ke wannan korafi, a gefe guda kuma malaman sun bayyana cewa sun kara wannan wa’adi ne duba da yadda gwamnati ta yi kunnen uwar-shegu da bukatunsu.

Kwamared Abdulkadir Muhammad, Shugaban Kungiyar ASUU reshen Arewa Maso Yamma, ya ce za su ci gaba da wannan yajin aikin ne domin su ba gwamnati lokacin da za ta iya biya musu bukatunsu.

“Mun ga cewar gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba wajen duba bukatunmu don haka muka ga cewar mu kara wadannan watanni don ba gwamnati lokacin da za ta iya warware matsalolin da ke tsakaninmu da ita.

“Muna fata zuwa wannan lokaci za a samu warwarewar lamurra.”

‘Ba don yajin aikin ba da jami’o’in Najeriya sun durkushe’

Da yake amsa tambayar Aminiya a kan dalilin da ya sa Kungiyar ASUU ba za su bi wata hanyar wajen neman biyan bukatunsu daga gwamnati ba sai yajin aiki, Shugaban Kungiyar ASUU reshen Jam i’ar Bayero Dokta Haruna Musa ya bayyana cewa kafin su dauki matakin yajin aikin sukan bi wasu hanyoyi na daban.

“Ya kamata mutane su fahimci cewa ba wai kawai yajin aiki ne kadai hanyar da ASUU muke bi ba. Kafin hakan mukan dauki matakai daban-daban da suka hada da tattaunawa da kai ziyarce-ziyarce wurin masu ruwa da tsaki. Ina tabbatar muku cewa yajin aiki shi ne mataki na karshe da muke bi wajen warware lamurra.”

A cewar Kwamared Musa yajin aikin da suke yi kwalliya tana biyan kudin sabulu.

“Yajin aiki yana kawo warwarewar matsalolin shi ya sa ma muke yin sa. Domin zan iya cewa yajin aikin ne ya sa gwamnati ta samar da Hukumar TETFUND haka kuma yajin aikin ne ya haifar da yanayin da jam’o’i ke samun damar tsayawa da kafafuwansu.

Ina tabbatar muku da cewa ba don yajin aikin ba da tuni jami’o’in sun dade da durkushewa kamar yadda makarantun firamare da sakandire na gwamnati suka durkushe a fadin kasar nan,” inji shi.

A nasa jawabin, Shugaban Kungiyar reshen Jama’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Haruna Mohammed Jibril, ya ce tafiya yajin aiki kamar alama ce da ke nuni da jiki na jin zazzabi, “kuma kamar yadda kowa ya sani ne sai mun bi matakai har kusan kashi uku kafin mu tafi yajin aiki,” in ji shi.

Ya ce “Ba mu fara ba sai da muka tattauna da shuwagabannin al’umma, har da shugabannin addinai da sarakuna.

“Wato gwamnati kamar ba da gaske take yi ba domin matsalar tana da yawa. Ka ga dai kudin gudanarwa da gwamnati ke ba Jami’ar ABU a shekara Naira miliyan 100 ne da ’yan kai kuma kudin wutar lantarki da jami’ar ke biya a shekara kusan Naira miliyan 100 ne, nawa ya rage, kuma idan na yi magana sai su ce wai ai dalibai na biyan kudin makaranta, kuma kudin makaranta da dalibai ke biya nawa ne?

“Don haka mu ba wai muna shiga yajin aiki don muna so ba ne, a’a, dole ce ta sa mu kuma al’umma su gane cewa muna bin duk wata hanyar da ta da ce kafin shiga yajin aiki kuma muna yi don su ne kawai ba don biyan bukatummu ba.”

Mun yi mamakin ci gaba da yajin aikin ASUU —Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta biya wa Kungiyar ASUU dukkan alkawuran da ta daukar mata a baya don ta janye yajin aikin gargadi da ta tsunduma na mako hudu.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne a matsayin martani kan tsawaita wa’adin yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in ta yi da mako takwas.

Minista a Ma’aikatar Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya yi wannan jawabin a tattaunawarsa da manema labarai a Abuja. Nwajiuba, ya ce Gwamnatin Tarayya ta biya dukkan bukatun ASUU, inda ya kara da cewa an saki dukkan alawus-alawus da sauran kudaden kungiyar da aka rike.

“ASUU ta kira taro kuma mun amsa gayyata tare da biyan dukkan bukatunsu, ciki har da alawusalawus da sauran kudadensu, amma ba mu san dalilinsu na tsawaita yajin aikin ba,” in ji shi.

Yajin ba zai magance matsalar ba —Bulama Bukarti

Da yake jawabi kan lamarin, lauya Bulama Bukarti ya yi rubuce-rubuce da dama a shafinsa na Facebook, inda a ciki yake sukar yanayin da Kungiyar ASUU din take amfani da hanya daya kawai wajen neman hakkinta, wato yajin aiki, hanyar da a cewarsa ba ta bullewa. A cewarsa, “daga 1999 zuwa yau, ASUU ta yi yajin aiki sau 16 na jimillar tsawon watanni 51.

A kowace shekara biyar, ASUU tana yajin kimanin shekara daya. Ke nan a kowace shekara biyar lakcara yana karbar albashin shekara daya ba tare da ya yi aiki ba.

Sannan kusan duk wanda ya gama jami’ar gwamnati a Najeriya, to ya yi asarar kusan shekara guda saboda yajin aiki.

’Yan siyasarmu ba su damu ba saboda ba sa tausayinmu. Su kuma ’yan ASUU sun gaza fito da hanyar da za ta bulle, wadda ba za ta cutar da dalibai ba.

“Lokacin da ina dalibi ban goyi bayan yajin aiki ba. Lokacin da na koyar ban goyin bayan yajin aiki ba. Kuma yanzu ma ba na goyon.

“Kuma wallahi da ASUU za ta ba wa kowa zabi, malamai da dama za su je su koyar da dalibansu. Dalili kuwa shi ne: wannan salo bai magance matsalar ba kuma yana cutar da dalibai.

“Mu cire son rai da kiyayya ko soyayya, mu ji tsoron Allah, mu duba gaskiya. Daga kin gaskiya, sai bata. Ita kuma gaskiyan nan ba ta bukatar ado.”

A wani rubutun daban, Bukarti ya ce, “Mu ba mu taba cewa kada ASUU ta nemi abin da take nema ba. Cewa muka yi yajin aikin bai yi aiki ba, saboda haka a hada kai da al’umma a yi amfani da wasu hanyoyin.”

Daga cikin hanyoyin da Bulama Bukarti ya kawo akwai gudanar da zanga-zangar lumana a duk fadin kasar, inda ya ce malamai da dalibai da iyaye za su fito su yi zanga-zangar, sannan a koma makaranta da rana a koyar da dalibai, duk da cewa wasu sun soke shi a kan wannan shawarar.