Rikicin aure: Sarkin Malamai ya gindaya sharadin janye kararsa
Sarkin Malaman Deidei Dokta Muhammad Alkandawi ya gitta sharadi ga ma’auratan nan da ya gurfanar a Kotun Sabo Wuse ta Jihar Neja kan zargin da a ke yi wa uwargida Adama na azabtar da abokiyar zamanta A’isha da ruwan zafi yayin da suke kokawa a gidansu da ke garin Dakwa, da kuma mijinsu Malam Isa […]
Sarkin Malaman Deidei Dokta Muhammad Alkandawi ya gitta sharadi ga ma’auratan nan da ya gurfanar a Kotun Sabo Wuse ta Jihar Neja kan zargin da a ke yi wa uwargida Adama na azabtar da abokiyar zamanta A’isha da ruwan zafi yayin da suke kokawa a gidansu da ke garin Dakwa, da kuma mijinsu Malam Isa Muhammad da ake zargi da yunkurin aikata ta’addanci ga Sarkin Malaman Deidei sakamakon ajiye amaryar magidancin a gidajensa don kulawa da ita.
Ma’auratan da aka tsare a babban ofishin ’yan sanda na Sabon Wuse, bayan an kai su kotun a ranar Alhamis da ta gabata sun fuskanci karar da Sarkin Malaman ya shigar ne ta hannun lauyansa.
bangaren Dokta Alkandawi ya bayyana niyyar janye karar a ranar, kuma alkalin kotun Mai shari’a danladi Usman Kutigi ya ba da damar sasantawa tare da bukatar da su koma washegari Juma’a. Magidancin ya wuce gida a yayin da aka ci gaba da tsare matarsa.
Sai dai a yayin da ya koma ofishin ’yan sandan a ranar Juma’ar da ta gabata da nufin kara zuwa kotun tare da matarsa, sai aka sake tsare shi, inda aka nuna masa takardar kamu daga kotu aka bukaci su rubuta takardar amincewa da aikata zargin da ake yi musu a matsayin sharadin sasantawa.
Rashin amincewa da hakan ne kuma ya sa a ka ci gaba da tsare su har zuwa yinin Talatar da ta gabata, magidancin da matarsa da ’ya’yansu hudu na tsare a ofishin. Koda yake sun koma kotun a ranar Litinin da ta gabata, amma zama a kan al’amarin bai yiwu ba saboda wasu dalilai, yayin da a ranar Talata da ta gabata kuma ba a kawo su kotun ba har lokacin da kotun ta tashi daga aiki.