Rikicin aure ya dabaibaye Sarkin Malamai

Wani Malami da ake yi wa lakabi da Sarkin Malaman Deidei, Dokta Muhammad Alkandawi da ke zaune a garin Dakwa ta bangaren Jihar Neja, ya maka wani magidanci tare da uwargidansa a kotu yana zarginsu da kokarin yin barazana ga rayuwarsa saboda ya dauki amaryar mutumin ya kai ta daya daga cikin gidajensa don kulawa […]

Rikicin aure ya dabaibaye Sarkin Malamai

Sarkin malaman Deidei Dokta Muhammad AlkandawiWani Malami da ake yi wa lakabi da Sarkin Malaman Deidei, Dokta Muhammad Alkandawi da ke zaune a garin Dakwa ta bangaren Jihar Neja, ya maka wani magidanci tare da uwargidansa a kotu yana zarginsu da kokarin yin barazana ga rayuwarsa saboda ya dauki amaryar mutumin ya kai ta daya daga cikin gidajensa don kulawa da ita a sakamakon kunar hannu da ta samu a yayin da take kokawa da abokiyar zamanta a gidansu na aure.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba ta makon jiya, a sakamakon sabanin da matan magidanci mai suna Mallam Isa Muhammad suka samu a tsakaninsu inda har ya kai su ga kokuwa, kuma a yayin fadan ne suka tuntsurar da wata tukunyar ruwan zafi da ke kusa da su, inda ya kona amaryar mai suna A’isha a hannu.
Bayan aukuwar lamarin, magidancin wanda ba ya gida a lokacin da lamarin ya faru, ya garzayo gida ya dauko wani ma’aikacin jinya wanda ya yi wa wadda ta konen magani, sai dai barinsa gidan ke da wuya sai amaryar ta garzaya gidan iyayenta da ke garin Deidei da ke kusa da garin na Dakwa. Daga can ne kuma aka kai ta wajen Malam Alkandawi, wanda yanzu haka yake daukar nauyin kulawa da ita.
Malamin dai ya kai maganar zuwa Ofishin ’Yansanda na garin Sabo Wuse ne a jihar Neja a ranar Juma’ar da ta gabata, daga can ne kuma ’yan sandan suka garzaya zuwa gidan magidancin inda suka yi awon-gaba da uwargidansa suka tsare ta a ofishinsu.
Sai dai daga bisani an bada belinta a ranar ga wani abokin mijinta mai suna Sirajo Salihu da nufin su koma ofishin a ranar Litinin da ta gabata, a ranar ne kuma mijinta, wanda tun farko ya bayyana bacin ransa ga surukinsa a kan zaman amaryar tasa a karkshin kulawar Sarkin Malamai ya je ofishin na ’yan sanda tare da abokin nasa da ya karbi belinta da kuma wani kaninsa mai suna Umar Aliyu tare da uwargidan.
Sai dai kuma zuwansu wajen ke da wuya sai aka tsare su gaba dayansu, kafin daga bisani aka saki mijin amma aka cigaba da tsare kaninsa da kuma uwargidansa a wajen, a yayin da shi kuma abokin nasa ya sulale.
Da wakilinmu ya tuntubi Sarkin Malamai ta waya akan korafin ajiye amaryar Malam Isa a wurinsa, sai ya ce ganin yanayin da matar ta ke ciki ne da kuma kusancinsa da iyayenta ya sa ya dauke ta ya kai ta asibiti inda aka yi mata magani, ya kuma dawo da ita gidansa domin cigaba da kulawa da ita. Y kara da cewa ya kai karar kishiyar matar ne saboda zaluntar abokiyar zamanta da ta yi. Ya kuma nemi a tuhumi mijin matan biyu da abokinsa akan barazana da su ka yiwa rayuwarsa da ikirarin afkawa dukiyarsa da ya ce sun yi.
Wakilinmu ya halarci zaman kotun a ranar Talata da ta gabata, inda aka gurfanar da uwargida Adama a kotun majistire da ke garin Sabo Wuse. A yayin zaman, jami’in kotun ya karanta bayanin zargi da ofishin ’yan sanda ya gabatar wa kotun, inda ake zargin uwargidan da aikata laifuka uku wadanda suka hada da laifin nuna karfi da cin mutunci da kuma azabtarwa. Sannan aka yi mata bayanin abin da aka zarge ta da aikatawa. Ta bukaci maida bayani, amma sai kotu ta sanar da ita cewa zaman ranar na matsayin karanta zargin binciken ’yan sanda ne, a zama na gaba ne wanda aka sa ranar Alhamis (jiya) za a saurari bangarorin biyu. A nan ne kuma mai sharia danladi Usman Kutigi ya bada umarnin a ci gaba da tsare ta har zuwa ranar Alhamis din don ci gaba da shari’ar.
Haka kuma an tuhumi mijin matar da abokinsa wanda ba a samu gurfanar da shi ba, da kuma kaninsa da ya dauke su da motarsa ta kabu-kabu zuwa ofishin ’yan sanda da aikata laifuffuka da suka hada da batanci da barazana ga rai da kuma yunkurin aikata ta’addanci ga Sarkin Malamai. Kotun ta bada umarnin su ma a tsare su har zuwa jiya Alhamis, ranar da za a ba su damar yin bayani ga kotu da kuma ci gaba da sauraron karar.
Ita dai uwargidan ana tsare da ita ne tare da wata ’yarta da take goyo, amma ita amaryar ba ta halarci zaman kotun ba a ranar, sai dai wani lauya da ya kasance a wajen a madadin Sarkin malamai da ya shigar da kararrakin biyu.