Rikicin bayan zaben 2011: Musulmin Kudancin Kaduna sun bukaci gwamnati ta biya su ragowar diyyar Naira biliyan hudu

Shugaban kungiyar Al’ummar Musulmin Kudancin Jihar Kaduna Alhaji Adamu Muhammed Kagarko ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta biya mutanen da rikicin bayan zaben 2011 ta shafa a yankin kudin diyyar Naira biliyan hudu da ya rage. Shugaban ya ce, gwamnatin ta yi alkawarin biyan su Naira biliyan bakwai ne, amma Naira biliyan uku kawai […]

Rikicin bayan zaben 2011: Musulmin Kudancin Kaduna sun bukaci gwamnati ta biya su ragowar diyyar Naira biliyan hudu

Shugaban kungiyar Al’ummar Musulmin Kudancin Jihar Kaduna Alhaji Adamu Muhammed Kagarko ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta biya mutanen da rikicin bayan zaben 2011 ta shafa a yankin kudin diyyar Naira biliyan hudu da ya rage.

Shugaban ya ce, gwamnatin ta yi alkawarin biyan su Naira biliyan bakwai ne, amma Naira biliyan uku kawai aka biya. Don haka sai ya ce akwai bukatar gwamnatin ta cika sauran kudin diyyar kuma ta hukunta wadanda suke da hannu a rikicin da ya lakume rayuka sama da dubu daya.

Shugaban Musulmin wanda kuma shi ne Marafan Kagarko ya ce sama da mutum dubu 200 ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin kuma har yanzu da yawansu ba su sake komawa gidajensu ba Kudancin Jihar.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai domin tunawa da ranar da aka yi rikicin na shekarar 2011 wadda kungiyarsu ta shirya. “Muna wannan taro ne domin tunawa da ’yan uwanmu Musulmi da aka kashe a Kudancin Jihar Kaduna a bayan zaben shekarar 2011. Akalla mutum dubu daya aka kashe kuma sama da dubu 200 suka rasa muhallansu,” inji shi.