Rikicin Billiri ya jawo asarar N500m —Gwamnati

Za a biya wadanda suka yi asara diyya don rage musu radadi.

Rikicin Billiri ya jawo asarar N500m —Gwamnati

Mazauna sun fake a saman duwatsu a yayin da garin ke ci da wuta a rikicin. Hoto: Rabilu Abubakar.

Rikicin kabilanci da ya rikide zuwa na addini a baya-bayan nan a garin Billiri na Jihar Gombe ya yi sanadiyyar asarar dakiyoyi na sama da Naira milian 500.

Rahoton kwamitin bincike don gano musabbabin tashin-tashinar da gwamnatin jihar ta kafa ne ya sanar da haka bayan kammala aikinsa.

A jawabinsa kan rahoton da kwamitin ya gabatar wa zaman Majalisar Zartarwar Jihar, Kwamishinan Yada Labaran Jihar Gombe, Julius Ishaya, ya ce wuraren ibada 33 ne aka kona wandada aka kiyasa a kan miliyan N33.1.

Kwamitin ya kuma gano mutum 41 da rikicin ya shafa da aka kashe wa Naira miliyan 94.6.

An kuma lalata shaguna 402 da wuraren kasuwanci 335 da shaguna mallakin karamar hukumar ta Billiri guda 66 wadanda kudinsu ya haura Naira biliyan 383.2.

Akwai kuma motoci da ababen hawa daban-daban da lambuna da aka salwantar, da kudinsu ya haura Naira miliyan 31.

Majalisar ta amince a abiya wadanda suka yi asarar diyya don rage musu radadin rayuwa.

Kwamishinan ya kara da cewa ita kanta Karamar Hukumar Billiri, an umurce ta da ta samar da wasu kudi dan a tallafawa.

An sanya dokar hana fita a wasu yankunan Taraba

Jami’an NSCDC sun daƙile harin ’yan bindiga a Kano

Matsalar Tsaro: Ku sayi makamai don kare kanku — Sarkin Argungun

Mai juna biyu na wata 8 ta shigar da ƙarar neman saki