‘Rikicin Boko Haram ya ci malamai 3,798 da makarantu 1,500 a Arewa maso Gabas’
Rikicin ya yi matukar kawo koma baya a harkokin ilimi a yankin Arewa maso Gabas.
Cikin tsawon shekara 12 da aka yi ana fama da rikicin Boko Haram, an kashe malaman makaranta 3,795 tare da kone makarantu akalla 1,500 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Babban Manajan Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC), Alhaji Mohammed Alkali ne ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da taron kara wa juna sani na kwana biyar ga malamai 300 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta Sa Kashim da ke birnin Maiduguri a Jihar Borno.
- An kama shi ya yi wa yara ’yan uwan juna fyade
- Farfesa Tanko Ishaya ya zama sabon Shugaban Jami’ar Jos
A cewarsa, harkokin ilimi sun samu koma baya matuka sanadiyar rikicin, wanda hakan ya sa ya zama tilas a rika shirya irin wannan bita don sake inganta harkokin koyo da koyarwa.
Ya kara da cewa, “sanin kowa ne faruwar wannan rikici ya yi matukar kawo koma baya a harkokin ilimin yankin Arewa maso Gabas duba da yadda aka samu yara da yawa sun kauracewa makarantunsu, sun koma gararanba a kan tituna tare da fadawa muggan dabi’u.”
Ya ce tsawon lokacin da wannan rikici ya dauka, matukar ba a dauki mataki ba akwai yiwuwar matasa maza da mata za su iya afkawa muggayen dabi’u.
Kan abin da ya shafi horar da malaman kuwa, Muhammad Alkali ya jaddada cewa akalla malaman makaranta kimanin 1,500 ne za a horar a cikin jihohi 5 a yankin Arewa maso Gabas.
Shugaban kamfanin kwararru na Limo Holdings Consult Lawan Alhaji ya bayyana cewa malaman makarantun firamare da kananan makarantun sakandare ne za a horar.