Rikicin Boko Haram ya ci rayukan dalibai 135 a Yobe
Rikicin Boko Haram ya ci rayukan daliban sakandare 135 da malamansu bakwai tare da jawo asarar dukiya ta akalla Naira biliyan 10 a Jihar Yobe tun fara rikicin a shekarar 2009.Kwamishinan Ilimi na Jihar Alhaji Muhammad Lamin ne ya bayyana haka a ganawarsa da Aminiya dangane da halin da bangaren ilimi ke fuskanta a jihar, […]
Rikicin Boko Haram ya ci rayukan daliban sakandare 135 da malamansu bakwai tare da jawo asarar dukiya ta akalla Naira biliyan 10 a Jihar Yobe tun fara rikicin a shekarar 2009.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Alhaji Muhammad Lamin ne ya bayyana haka a ganawarsa da Aminiya dangane da halin da bangaren ilimi ke fuskanta a jihar, bayan barkewar rikicin Boko Haram.
Alhaji Muhammad Lamin ya kara da cewa a duk tsawon lokacin da aka dauka ana rikicin a jihar, bangaren ilimin ya fi kowane fanni fuskantar wahalhalu tun daga kan kashe dalibai da malamansu da ba su ji ba, ba su gani ba, ga kuma kone gine-ginen makarantu da sace kayayyakin koyo da koyarwa da aka kiyasta kudin akalla Naira biliyan 10.
Kwamishinan ya ce fatarsu a samu ingantuwar hanyoyin kudin shiga ta yadda gwamnatin jihar za ta samu gyaggyara irin barnar da jihar ta fuskanta daga ayyukan ta’addancin ’yan kungiyar Boko Haram.
Kwamishinan ya roki Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin ba da tallafi na kasashen duniya su tallafa wa jihar musamman bangaren ilimi domin a samu a gyara barnar da aka yi cikin hanzari don harkokin ilimi su inganta a jihar.
Alhaji Muhammad Lamin ya kuma nemi iyaye da daliban makaratu da kuma malamai su ci gaba da nuna juriya game da wannan lamari inda ya ba su tabbacin cewa gwamnatin jihar da taimakon Allah da kuma
jajircewar jami’an tsaro za ta samar da cikakken tsaro a makarantun, don haka kada su yi kasa a gwiwa wajen tura ’ya’yansu makaranta.
Ya ce duk da matsalolin karancin kudi da gwamnatin ke fuskanta za ta ci gaba da biyan kudin jarrabawar kammala makarantar sakandare (WAEC da NECO) ga daliban jihar kamar yadda ta saba tare ba da ilimi kyauta.