Rikicin Boko Haram ya durkusar da harkar ma’adinai -Shugaban mahaka ma’adinai

Aminiya ta gana da shugaban kungiyar masu harkar ma’adinai na kasa, Alhaji Sani Shehu, inda ya bayyana yanayin da harkar ke ciki a halin yanzu. Aminiya:  Za mu so ka gabatar mana da kanka.Alhaji Sani Shehu:  Sunana Alhaji Sani Shehu, shugaban kungiyar mahaka ma’adinai na Najeriya, wadda ta kunshi kamfanoni da ke aikin hakar ma’adinai […]

Rikicin Boko Haram ya durkusar da harkar ma’adinai -Shugaban mahaka ma’adinai

Aminiya ta gana da shugaban kungiyar masu harkar ma’adinai na kasa, Alhaji Sani Shehu, inda ya bayyana yanayin da harkar ke ciki a halin yanzu.

Aminiya:  Za mu so ka gabatar mana da kanka.
Alhaji Sani Shehu:  Sunana Alhaji Sani Shehu, shugaban kungiyar mahaka ma’adinai na Najeriya, wadda ta kunshi kamfanoni da ke aikin hakar ma’adinai da ma’aikata da kuma ’yan kasuwa. kungiyar ta fara ne a matsayin ta leburori masu aiki da kamfanoni da ke hakar ma’adinai na Turawa, wadda aka yi wa rajista a shekarar 1944. A lokacin Turawa ne kadai ke da izinin gudanar da harkar, inda ’yan kasa kuma ke aiki a matsayin leburori. To, bayan an samu ’yanci a shekarar 1960, sai ’yan kasa suka fara, har dai zuwa yanzu da suka gaje harkar gaba daya.
Gwamnati ce ke ba da lasisin harkar, wanda ya kunshi na nemansa da na hakarsa, sai kuma na masu saya da sayar da shi. Mambobinmu na zuwa ne daga rukunin wadannan mutane uku bayan sun samu lasisi ta hannun ma’aikatar kula da ma’adinai. Daga cikin aikace-aikacen kungiyar akwai kare kudurorin mambobinta da nema musu hakki da kuma bukatar sauya dokar da muka fahimci tana da illa a harkokinmu.
Aminiya: Daga cikin abubuwan da kuke aiki da su akwai abubuwan fashe-fashe (nakiya), yaya kuke ji a wannan lokacin da mallakar irin wadannan abubuwan ya saba wa doka?
Sani Shehu: Lallai aikinmu sai an hada da nakiya, amma Alhamdu lilLahi, tunda wannan bala’i ya fara ba a taba kama wani mambanmu da nakiya ba a bisa ka’ida ba. Duk wanda ka gani da nakiya, to ya cika sharadi da ka’idojin da ma’aikatar kula da ma’adinai ta shimfida. Sai dai idan ana maganar wadanda suka fi fuskantar matsalar tawayar harkoki a wannan lokaci ne, to mahaka ma’adinai su ne a gaba. Na farko dai karfin kasuwar ma’adini yana kasar waje ne; na biyu, wannan harka idan ana so a samu nasararta, kamar yadda take a ko’ina a duniya, sai an hada da Turawa, to Turawan nan a yanzu gudunmu suke yi, saboda a duk lokacin da aka ce nakiya ta tashi a wani gari a kasar nan, dimbin wadanda ke da shirin zuba jari muke rasawa. Na je kasashe kamar su China da Thailand da Dubai wajen neman wadanda za su zo mu hada hannu, amma wadanda suka zo ba su da yawa, kuma ko su din ma da suka zo har yanzu ba su sa hannu ba.
Aminiya: Wadanne irin ma’adinai ne kasar nan take ji da su baya ga fetur?
Sani Shehu: Allah Ya albarkaci kasar nan da tarin ma’adinai, musamman ma a bangarenta na Arewa. Za a iya raba su kamar kashi uku: akwai masu yanayin duwatsu da tama da karafa; sai kuma ma’adinai masu yanayin kasa da ake sarrafa su a masana’antu, kamar farar kasa da jifsin na siminti, da dai sauransu. Sai dai kash!, bayan bayyanar man fetur gaba dayan wadannan ma’adinan sun daina samun cikakkar kulawar gwamnati.
Aminiya:  Amma ana yi wa bangaren Arewa gori a matsayin wadda ba ta tallafa wa asusun kasa duk da wannan dimbin ma’adinai da ka ce tana da shi.
Sani Shehu:  A duk lokacin da na ji ana yi wa Arewa gori a matsayin wadda ba ta tallafawa ta fuskar asusun kasa murna nake yi, saboda ina sa rai wannan gorin zai sa su zucciya su yunkuro su sanya jari ta fuskar ma’adinai don inganta arzikin Arewa da kasa baki daya. Ai a baya Arewa ta tallafa a bangaren ma’adinai da kayan gona da kuma da kuma fatu da kiraza, wanda shi ne dukiyar da aka yi amfani da ita wajen hako man da ake tinkaho da shi a yanzu. A shekarar 2008 na gabatar da kasida a wani wajen taro na gwamnonin Arewa inda na bukaci su rika cire ko da kashi daya daga cikin dari na kudin da suke samu don bunkasa wannan harka. Harkar ma’adini ba a fara cin gajiyarta take-yanke, sai an shekara kamar biyar, hakan zai tallafa musu wajen rage dogaro a kan asusun kasa, sannan kuma ya samar da dimbin aiki ga al’ummarsu.
Aminiya: Ya ake fara zuba jari a harkar?
Sani Shehu: Da farko za a binciko inda ake da ma’adini, sai a tantance yawansa da ingancinsa da kimar wahala ko sauki wajen kaiwa gare shi da darajarsa, sai kuma inda za a sayar da shi da kuma yadda za a rufe wajen da aka hake shi bayan an kwashe albakatu, sai kuma tantance na wane waje ne zai fi saukin samuwa, sannan kuma na wane wajen ne zai fi ba da kudi da kuma karancin hadari. To bayan ka kammala wannan sai ka yi nazari a kan ribar da zai bayar. Wannan al’amari duk ya shafi kimiyya, wanda bai yiwuwa sai da zuba kudi kuma ta hanyar sadaukarwa. kungiyarmu a shirye take wajen ba su shawarwari da kuma sirrin harkar.
Aminiya: Wace jiha ce ta fi albarkar ma’adinai a Arewa?
Sani Shehu: A hasashe da kuma aikace-aikace da ake yi wanda ba wai cikakken bincike ne aka yi a kan  al’amarin ba, Jihar Zamfara ce ta fi yawan ma’adinai a Najeriya baki daya, sai dai fa ka sani kowace jiha a kasar nan tana da ma’adinai, amma jihohin Arewa ne suka yi fintinkau.
Aminiya: Mahakan ma’adinai, musamman a Jihar Zamfara sun yi ta fuskantar matsalolin rashin lafiya masu nasaba da aikinsu, mene ne ya jawo hakan?
Sani Shehu: Babban dalili shi ne rashin bin ka’idar aikin a sakamakon rashin abun hannu da kuma rashin sanin makamar aiki, wanda ya kunshi tantance hadarinsa da kuma yadda mahakin zai kare lafiyarsa da na mazauna wajen, wanda masana ke ba da shawara a kan yadda za a tunkare shi, saboda yawancin sinadarai (chemical) da kake ganin ana hadawa daga ma’adinai ake samunsu. Sai dai, alhamdu lilLahi, bayan faruwar matsalar gwamnatin tarayya da kungiyoyin duniya da kuma tamu kungiyar mun same su muka ba su shawarwari ta hanyar taron bita da aka rika shirya musu.
Aminiya: Wace kasa ce a duniya ta ci gajiyar ma’adinanta da Najeriya za ta iya koyi da ita?
Sani Shehu: Akwai Afirka ta Kudu da Ghana da Mozambik da Saliyo da kuma Nijar, duk wadannan kasashen tattalin arzikinsu ya ta’allaka ne a kan ma’adinai, in ban da kasar Nijar da ta gano mai a ’yan shekarun nan, amma a baya ma’adinin ‘uranium’ ne kawai ta dogara da shi.