Rikicin Boko Haram ya jawo kuncin rayuwa a Kamaru
Kusan shekara guda ke nan da ’yan kungiyar Boko Haram suka fara yin kutse a jamhuriyar Kamaru harkokin kasuwanci suka fara ja da baya. Ya kasance ’yan kasuwa mazauna arewacin kasar wadanda duka harkokinsu suka ta’allaka akan ketarawa Najeriya domin su sayo wasu kayayyaki, a yanzu hakan ya gagara, hakan kuma a dalilin rashin tsaro […]
Kusan shekara guda ke nan da ’yan kungiyar Boko Haram suka fara yin kutse a jamhuriyar Kamaru harkokin kasuwanci suka fara ja da baya.
Ya kasance ’yan kasuwa mazauna arewacin kasar wadanda duka harkokinsu suka ta’allaka akan ketarawa Najeriya domin su sayo wasu kayayyaki, a yanzu hakan ya gagara, hakan kuma a dalilin rashin tsaro sanadiyyar aikin ta’addancin da ’yan kungiyar Boko Haram suke ta rubanyawa. Alhalin kuma yankin arewacin Kamaru ya dogara ne da samun kayayyakin da suke shigowa daga Najeriya kamar su kayan miya da yadudduka da atamfofi da man fetur da sauransu.
Har ila yau, masu yawon bude ido masamman Turawa sun kaurace wa wannan yankin a dalilin yawaita yin garkuwa da fararen fata da ake yi. Akan haka ne akasarin ofisoshin jakadancin wasu kasashen Yammacin Duniya suka tsawatar wa ’yan kasarsu da su kaurace wa kai ziyara arewacin Kamaru. Hakan kuma ya kara tsananta ne lokacin da aka yi garkuwa da wasu ’yan kasar China su 10 lokacin da suke aikin gina hanyar mota. Kodayake bayan ’yan kungiyar Boko Haram sun sake su. An samu cimma wata yarjejeniya tsakanin gwanatin Kamaru da kuma ta Chaina domin wadannan ’yan kwangilar su dawo su koma bakin aiki.
Bugu da kari, jama’a na fama da matsalar rayuwa a yankin arewacin Kamaru. Sun koma fuskantar tsadar man fetur a gidajen sayar da su, a wasu lokutan kuma ma ana samun karancin man a dalilin cunkoson da ake yi motoci da kuma babura, alhalin kuma man daga kudancin ake daukowa. Hakan na nufin sai an dauki lokaci gabannin ya isa arewaci.
Wata babbar matsalar da take addabar al’ummar wasu kananan Hukumomin lardin Arewa Mai Nisa kamar su Darak da Blangoua da Dabar Tsamiya da sauransu. Saboda hani kwata-kwata da Hukumomi suka yi musu na yawo da babura, ga shi kuma babu motoci a wadannan garuruwa. Hakan ya sa jama’a yin amfani da kafarsu wurin tafiya duk inda suka nufa kamar gonaki da makarantu da asibiti da sauran wurare. Hanin da har a yanzu ba a kai da bayyana wa’adinshi ba, na ci gaba da hana mutane sa da zumunta a tsakaninsu.
Bayan rikicin Boko Haram, bullar annobar Ebola a jihar Legas ta Najeriya ya sa Gwamnatin Kamaru ta rufe duka iyakokinta da kasar. Wannan ya sa al’amura suka dada cakudewa. Har ila yau, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana cewa Najeriya ta kawo karshen annobar, hakan ya sa Kamaru ta sake bude iyakokinta, inda masana ke cewa hakan zai traimaka wajen sanya al’amura komawa yadda suke.