Rikicin Boko Haram ya jawo wa Jami’ar Maiduguri babbar matsala – Farfesa Njodi
Shugaban Jami’ar Maiduguri Farfesa Ibrahim A. Njodi, ya ce rashin tsaron da ake fama da shi a Maiduguri sakamakon hare-haren ’yan Boko Haram ne babban kalubalen da jami’ar ta gamu da shi a shekarun baya.Farfesa Ibrahim Njodi ya yi furucin ne yayin da yake jawabi a wurin taron kaddamar da littafi mai suna: ‘Elementary Marketing […]
Shugaban Jami’ar Maiduguri Farfesa Ibrahim A. Njodi, ya ce rashin tsaron da ake fama da shi a Maiduguri sakamakon hare-haren ’yan Boko Haram ne babban kalubalen da jami’ar ta gamu da shi a shekarun baya.
Farfesa Ibrahim Njodi ya yi furucin ne yayin da yake jawabi a wurin taron kaddamar da littafi mai suna: ‘Elementary Marketing for Senior Secondary School’ wato ‘Matakin Farko na Ilimin Kasuwanci don ’Yan Makarantar Sakandare’ da aka gudanar a makarantar gwamnati ta Tudun Wada da ke Abuja.
Ya ce, “Babbar matsalar da muka fuskanta a shekarun baya ita ce ta rashin tsaro sakamakon ayyukan ’yan Boko Haram. Har sai da ta kai mun kusa rufe jami’ar amma da taimakon Allah sai muka yanke shawarar mu ci gaba da karatu don kada mu bai wa ’yan ta’adda dama su rika ganin sun samu galaba. Domin idan mun rufe jami’ar ina daliban da malaman za su je? Sai kawai muka tsaya muka jajirce har lokacin da al’amura suka yi sauki a yanzu. Da a ce mun rufe makaranatar da su kansu jami’an tsaro da suka ba mu gudunmawa ba su samu kwarin gwiwar taimaka mana ba. Amma yanzu komai ya lafa abubuwa na gyaruwa.”
Farfesa Njodi ya ce jami’an tsaro sun hada gwiwa da jami’an tsaron cikin jami’ar kuma hadin kan da aka samu ya taimaka kwarai da gaske wajen samar da tsaro da ba da kariya ga dalibai da ma’aikatan jamai’ar baki daya.
Ya cewa rashin tsaron ya shafi batun daukar dalibai a jami’ar inda wasu iyaye da daliban su kansu ba sa son zuwa Jami’ar Maiduguri. “Shi ya sa saboda karancin dalibai ba mu yi jarrabawar tantance dalibai da jami’o’i suke yi ba sai kawai muka bai wa wadanda suke son shiga jami’ar gurbin karatu ba tare da wata matsala ba,” inji shi.
Shugaban ya ce tsaikon da aka samu wajen bayar da takardar shaidar kammala jami’ar ya faru ne saboda sakacin da aka samu. To amma yana kama aiki ya lura da matsalar tare da magance ta cikin gaggawa. “Da na fahimci cewa matsalar za ta shafi martabar jami’ar sai muka dauki matakan da suka dace na ganin an gyara al’amarin. A yanzu duk wanda ya kammala jami’ar daga shekarar 2002 zuwa 2014 ya zo ya karbi takardar shaida kammala karataunsa a Jami’ar Maiduguri,” inji shi.