Rikicin Boko Haram ya rutsa da mutum miliyan uku – NEMA
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta ce rikicin Boko Haram da ya fi kamara a yankin Arewa maso Gabas ya shafi akalla mutum miliyan uku a yankin.Kuma Hukumar NEMA ta ce daga watan Junairu zuwa watan Maris na bana, kimanin mutum dubu 250 ne suka rasa muhallansu a jihohin Borno da Yobe da […]
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta ce rikicin Boko Haram da ya fi kamara a yankin Arewa maso Gabas ya shafi akalla mutum miliyan uku a yankin.
Kuma Hukumar NEMA ta ce daga watan Junairu zuwa watan Maris na bana, kimanin mutum dubu 250 ne suka rasa muhallansu a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.
Shugaban Hukumar NEMA, Alhaji Muhammad Sani Sidi ne ya bayyana haka inda ya ce a Jihar Borno lamarin ya rutsa da fiye da mutum miliyan daya da dubu 300, a yayin da fiye da mutum miliyan daya musamman mata da yara da kuma tsofaffi lamarin ya rutsa da su a Jihar Adamawa.
Alhai Sani Sidi ya ce, a Jihar Yobe inda aka rika kashe daliban makarantu, rikicin ya rutsa da fiye da mutum dubu 770.
Hukumar NEMA ta ce ta samu wadannan alkaluma ne bayan wani aikin hadin gwiwa da ta gudanar tare da kungiyar agaji ta Red Cross da kuma kungiyoyin agaji na jihohin da abin ya shafa.
Binciken da hukumomin suka gudanar ya nuna cewa a yanzu haka galibin mutane a yankin Arewa maso Gabas ba sa iya samun abinci sau uku a rana.
kungiyar Boko Haram wacce ta addabi yankin, ta kashe dubban mutane tare da kone dukiyoyin al’umma, inda ta zafafa kai hare-hare a watanni uku na farkon wannan shekara, tana kashe jama’a tare da kone kauyukan da harinta ya isa gare su.
A makonni biyu da suka gabata sojoji sun ce sun tarwatsa sansanin ’ya’yan kungiyar a dajin Sambisa, sai dai kuma daga baya ’ya’yan kungiyar sun yunkuro inda suka kai hari harin barikin soja na Giwa da ke garin Maiduguri da niyyar kubutar da ’ya’yan kungiyar da suke tsare a can, lamarin da ya jawo mutuwar kusan mutum 500 da galibinsu fararen hula da ke tsare da aka zargi sojoji da kashe su. Daga baya kungiyar Boko Haram ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna cewa ta samu nasarar kubutar da ’ya’yanta da ke tsare a barikin.
Duk da cewa jihohin uku na karkashin dokar ta-baci na tsawon watanni hakan bai kawo karshen zubar da jinin da ake yi ba.